An sanya ranar fara rubuta jarrabawar Jamb 2020

An sanya ranar fara rubuta jarrabawar Jamb 2020

Hukumar shirya jarrabawar Jamb UTME ta bayyana cewa za’a fara rubuta jarrabawar ta shekarar 2020 a ranar 14 ga watan Maris zuwa ranar 4 ga watan Afrilu na shekarar ta 2020.

Shugaban hukumar shirya jarrabawar Jamb din ta kasa Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin dinnan jim kadan bayan gama ganawarsu da masu ruwa da tsaki game da jarrabawar a birnin tarayya Abuja.

Mr. Oloyede yace za’a fara rijistar jarrabawar ne ga dalibai a ranar 13 ga watan Janairu zuwa ranar 17 ga watan Fabrairu na shekara mai kamawa ta 2020.

Kazalika ya kara da cewa dalibai zasu rubuta jarrabawar share fage mai lakabin (Jamb Mock) a ranar 18 ga watan Fabrairu na shekara ta 2020 din.

Muna fatan Allah ya baiwa dalibai sa’a.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!