Kun san jami’ar gwamnati da ake samun Admission ba tare da Jamb ba?

Kun san jami’ar gwamnati da ake samun Admission ba tare da Jamb ba?

Mecece NOUN?

National Open University (NOUN) wadda ake kira da jami’ar karatu daga gida, jami’a ce da gwamnatin tarayya ta samar domin baiwa dalibai damar yin karatu daga gida.

national open university courses

Abun nufi dai duk inda kake a kasar nan zaka iya karatu a jami’ar, kana iya zabar irin abun da kake son nazarta wato Course sai kuma ka cike darusan tsangayar da kake son yin nazari suka ware maka duk a zangon karatu wato Semester.

Idan dalibi yana cikin karatu kuma sabgoginsa na rayuwa suka yi masa yawa, to kana da dama ka tsayar da karatun har zuwa sanda ka samu damar cigaba da yi, ba tare da samun wata matasala ba ko tsaiko.

A ina jami’ar NOUN ta ke?

Jami’ar NOUN tana da cibiyoyi a ko ina a Najeriya kama daga yakin kudancin kasar zuwa Arewaci ko yankin gabashi zuwa yammaci, a nan yankin mu jami’ar na da rassa a jihohin Kano da Kaduna da kuma Jigawa.

Shiga nan domin ganin sauran wuraren da jami’ar take da cibiyoyi

Matakan karatun da ake yi a NOUN

  1. Ana karatun Diploma irin wadda ake yi a makarantu irin su Polytechnic da FCE.
  2. Ana yin Bsc, wato digiri na farko.
  3. Ana yin Postgraduate Diploma, ta share fage kafin tafiya digiri na biyu.
  4. Sannan ana yin Master’s Degree, wato digiri na biyu.
  5. Haka kuma ana yin karatun PhD, wato digiri na uku ko digirin digir-gir.
  6. Sannan ana yin karatun HND, PGD da sauransu.

A wannan jami’ar ne tsohon shugaban kasa Olu Segun Obasanjo yayi digirin san a uku wato PhD.

Ku biyo mu a rubutu na gaba domin samun cikakken bayanai akan wannan jami’ar ta NOUN.

Rubutu masu alaka:

[Kayi Register] Karatu kyauta akan Media and Information Literacy a National Open University

Legal Kano ta fara sayar da form na NCE, Pre-NCE da Diploma

Shirin “Kwana Casa’in” na neman sabuwar jaruma

An fara sayar da form din NCE, IJMB da Remedial na makarantar CAS Kano

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!