Shirin “Kwana Casa’in” na neman sabuwar jaruma

Shirin “Kwana Casa’in” na neman sabuwar jaruma

Gidan talabijin na Arewa 24 kafar yada labaran Hausa mafi yawan mabiya a duniya ta sanar da cewa tana neman sabuwar jaruma wadda zata taka rawa acikin fitaccen film din nan nata mai nisan zango wato “Kwana Casa’in”.

Shirin “Kwana Casa’in” dai shiri ne da yake duba kan zamantakewar al’ummar mu, musamman a bangaren gudanar da mulki.

Jarumar da Arewa 24 ke nema a shirin ita ce mai shekaru 50 zuwa 60.
Farar fata kuma mara jiki sosai wato dai ba baka ba kuma ba ‘yar lukuta ba.
Mace mai kwarjini da dattako.
Sannan bakuwar fuska wadda ba ta saba fitowa a fina-finai ba.

Mai sha’awa sai taje harabar gidan talabijin na Arewa 24 ranar jumu’a 22 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Domin karin bayani sai ku ziyarci shafin Facebook na Arewa 24.

Allah ya bada sa’a.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!