[Da dumi-duminsa] SUBEB ta dage jarrabawar masu neman aikin koyarwa da ta shirya gobe Laraba

Home Government Issues [Da dumi-duminsa] SUBEB ta dage jarrabawar masu neman aikin koyarwa da ta shirya gobe Laraba
[Da dumi-duminsa] SUBEB ta dage jarrabawar masu neman aikin koyarwa da ta shirya gobe Laraba

[Da dumi-duminsa] SUBEB ta dage jarrabawar masu neman aikin koyarwa da ta shirya gobe Laraba

Hukumar ilimi bai daya ta jihar Kano wato SUBEB na sanar da daukacin wadanda suka nemi aikin koyarwa karkashin hukumar cewa, hukumar ta dage gabatar da jarrabawar data shirya musu a gobe Laraba sakamakon yawan mutanen da suka nemi a daukesu aikin na koyarwa.

A yanzu hukumar zata gabatar da jarrabawar a ranar Alhamis 29, ga watan Agustan da muke ciki (2019), a matakin shiyyoyin ilimi, za’a fara da shiyyar Nassarawa wadda take da kananan hukumomi hudu 4 wadanda suka hada da Nassarawa, Fagge, Tarauni, da Dawakin Kudu.

Karamar hukumar Fagge zasu yi jarrabawarsu a kwalejin shari’a ta Malam Aminu Kano wato Legal.

Inda kananan hukumomin Nassarawa, Tarauni da Dawakin Kudu kuma zasu yi tasu a Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi dake Kumbotso.

Hukumar tana kira ga sauran kananan hukumomin da su cigaba da jiran sanarwa ta gaba.

Mun samu sanarwa daga mataimakin darakta mai kula da hurda da jama’a na hukumar ilimi bai daya ta jihar Kano Malam Balarabe Danlami Jazuli a madadin shugaban hukumar Dr. Danlami Hayyo.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

An fara Sayar da Form na Makarantar Institute of Corporate Security and Intelligence Study

Me Yakamata Kayi Bayan Post UTME ta Fito?

Cibiyar Ilimi ta Mafatihul Khair dake Kano Tana Neman Ma’aikata

An Fara Sayar da Form na Karatun OUTREACH na Kwalejin Audu Bako dake Kano

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!