Nayi Changing Course zuwa BUK amma rijistar Post-UTME din yaki yi, shin ko meye matsalar?

Home Admission Nayi Changing Course zuwa BUK amma rijistar Post-UTME din yaki yi, shin ko meye matsalar?
Nayi Changing Course zuwa BUK amma rijistar Post-UTME din yaki yi, shin ko meye matsalar?

Nayi Changing Course zuwa BUK amma rijistar Post-UTME din yaki yi, shin ko meye matsalar?

ASOF. QUALITY ASSURANCE COMMITEE 2019.

 • Nayi Changing Course zuwa BUK amma rajistar Post-UTME din yaki yi, mai yasa?
 • Na cika Awaiting Results shin zan iya yin Rajistar Post-UTME na BUK?
 • Shin idan inada NBAIS zan iya neman Kowanne Course a BUK?

Kungiyar Arewa Students Orientation Forum tayi Nasarar tattaunawa da Admission officer na Bayero University, kano a ofis dinshi a safiyar yau, inda ya amsa mata wasu tambayoyi dakuma Karin haske akan wasu abubuwan da suka shafi admission na Shekarar 209/2020, ga yadda tattaunawar ta kasance bayan wakilin ASOF din ya gabatar da kanshi, ga admission officer din: –

 • ASOF: – Ranka ya Dade, akwai daliban mu dasukayi Changing of Course and Institution zuwa Jami’ar tq Bayero amma kuma rajistar Post-UTME din baya yi, ko a ina matsalar take?
 • ADMISSION OFFICER: – Eh hakane bazaiyi ba, dalili kuwa Shine saboda bamu Riga munyi downloading Data dinsu ba, bare mu turashi CIT Wanda hakan ne zai basu damar Yin rajistar ta Post-UTME, amma Insha-Allah gobe zamuyi downloading Data din nasu, Saboda haka Ku gaya masu cewa daga gobe zasu iya gwadawa sugani Insha-Allah zaiyi.
 • ASOF: – to kenan idan kukayi downloading Data din gobe, shikenan bazaku kara yi ba?
 • ADMISSION OFFICER: – a’a ba mun gama ba kenan zamu karayi acan tsakiya, sannan kuma acan karshe ma zamu kara yi.
 • ASOF: – OK, to ranka ya Dade danganeda masu Jarabawar NBAIS ASOF tanada masaniyar cewa kusan Shekara uku kenan zuwa hudu bakowanne course ne jami’ar Ku take bawa masu jarabawar NBAIS ba, shin har yanzu akan haka ake ko an samu canji?
 • ADMISSION OFFICER: – a’a kamar yadda kuka sani BUK bata bawa masu NBAIS Kowanne course, to har yanzu hakan yake, ba’a bayarwa, Course dinda kawai zaka iya karantawa da NBAIS Result dinka indai anan BUK ne Shine;

B.A Islamic Studies, kokuma B.A Arabic. Saboda haka ko B.A Hausa, ko B.A (Ed) bazaka iya karantawa ba indai anan BUK ne, bare kuma Law kokuma wasu science Courses koda kuwa ka hada duk requirements dinda course din yake bukata

 • ASOF: – Good, to ranka ya Dade, daliban da sukayi applying BUK amma kuma awaiting results ne to su menene matsayinsu danganeda Post-UTME?
 • ADMISSION OFFICER: – Basuda wata Matsala, zasu iyayin rajistar Post-UTME dinsu, duk lokacinda Result din ya fito sai suje suyi Uploading, babu matsala suje suyi rajistar Post-UTME din su kawai.
 • ASOF: – danganeda Diploma, a DE wanne ne kuke amsa?
 • ADMISSION OFFICER: – eh National Diploma (ND) kawai muke amsa, Sai kuma IJMB, kokuma NCE.
 • ASOF:- Ranka ya Dade alokacin Admission Screening Exercise ASOF ta ziyarci wuraren da akeyi, inda taga cewa kunada wani guideline da kuke amfani dashi wajen Qualifying kokuma Disqualifying na Candidate, shin ko ASOF zata iya samun Copy din guideline din ?
 • ADMISSION OFFICER:- a,a gaskiya a yanzu bazan iya Baku ba saboda Official ne, amma zan tattauna da hukumar gudanarwa idan ta yarda a Baku to zan Baku Insha-Allah
 • ASOF:- Shin idan mutum yayi applying BUK ta DE kokuma ta JAMB sai bayan ya cire slip dinshi na Post-UTME saikuma yaga bazai samu admission a wannan Course din ba, shin zai iya canjawa bayan kuma ya Riga yayi rajistar Post-UTME din kokuma yq cire Slip dinshi na DE ?
 • ADMISSION OFFICER:- gaskiya banida amsar wannan tambaya taku saidai kuje Ku nemi Director CIT saboda Sune suke kula da bangaren.
 • ASOF:- OK, to mungode Ranka ya Dade, muna fatar zaka kara bamu dama irin wannan idan bukatar hakan ta taso !
 • ADMISSION OFFICER:- babu matsala, kofata a bude take aduk lokacinda kuka bukaceni, babu wata matsala Insha-Allah. Ga lambar wayata kuma in case koda akwai wani Abu na gaugawa saiku kirani 080988……………
 • ASOF:- to Mungode, Atashi lafiya
 • ADMISSION OFFICER:- nima na gode, a sauka lafiya.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Sanarwa] Za’a fara register Post UTME na Jami’ar FUD Dutse

An fara sayar da form na International University of Languages (iUOL)

Za’a fara Register Post UTME a Federal University Dutsinma (FUDK)

BUK Zata Fara Screening ga Masu D.E

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!