Na cika sharudan da makaranta ke bukata, amma banga sunana a admission list ba?

Home Admission Na cika sharudan da makaranta ke bukata, amma banga sunana a admission list ba?
Na cika sharudan da makaranta ke bukata, amma banga sunana a admission list ba?

Na cika sharudan da makaranta ke bukata, amma banga sunana a admission list ba?

Arewa Students Orientation Forum.

Quality Assurance Committee

(2019/2020 Admission)

Matsaloli:

» Nacika Dukkan Sharadin da Jami’a Take Buqata Amma Sai Naga Babu Sunana a List Din Admission.

»Har Anbani Admission Nazo Wajen Screening Sai Aka Kwace

» inada Wata Matsalar Da nakasa Gane Hanyar Dazan Magance ta.

Matsala Tafarko:

Nayi JAMB Naci Adadin Maki din Da’ake Buqata, Nayi POST UTME Shima Naci Adadin Maki Mark din Da’ake Buqata Amma ban Samu Admission ba

Koda Yaushe, Dalibi kanyi Tunanin Cewa ko Dan Bashi da Hanya ne Yasa Makarantar Dayake Nema Bata Bashi Admission ba, a Zahirin gaskiya Wani Lokacin abun Bahaka yake ba,

Babbar Matsalar itace Rashin Sanin Dukkan Ka’idojin da Makarantar Ta Shimfida kafin Ta Baka Admission, Kowacce Jami’a Dubban Mutane ne Suke Neman ta Ammafa duk da Yawan Mutanen bakowa ne Yake Cika Sharadin Samun Admission din ba.

Abu Nafarko Yakamata Kafara Dubawa Shin Wadanna Ka’idojin Makarantar ka ta Shimfida kafin bayar da Admission a Matakin UTME/JAMB Kokuma D.E?

So Dayawa Dalibi Kan Nemi Wani Course din da Mark din sa Bekai ba Alhalin da Ya Canja zuwa wani Course din da Sai Abashi.

A Bangaren Masu D.E Kuwa Matsalar Tafi Yawa a Shekarar da Ta Gabata committeen ASOF. Yaci Karo da Dalibai Dayawa a Jami’oi Dayawa Wanda Awajen Screening aka Kwace Admission Dinsu da ASOF. Tayi Bincike Tagano Dayawa daga Cikin Su, Sunyi Private Diploma ne Wacce ba Karbabbiya Bace a Wannan Jami’ar Yayin da Wasu Kuma Result/CGPA dinsu ne Yayi Low.

Tabbas Akwai Abubuwan Dubawa Dayawa kafin Kadawo Gida ka Zauna Zaman Jiran Admission.

Abubuwan Dubawa:

» Nawa Kaci a JAMB?

» Nawa Kaci a POST UTME?

» Yaya Result Dinka Na NECO/WAEC Yake?

» Nawa Ake Nema a Department Dinka?

» A’Level Dinka Lower ne?

» Kana da Matsala ta Banbancin Suna a Takaddun ka?

» Wacce Matsalar Kake Tunani Bayan Wannan?

Sanin amsar Wadannan Tambayoyin ne Kadai zai Baka Damar Magance Matsalar ka ASOF. Ashirye take ta Taimaka Ta Kowanne Bangare.

A Matsayin Mu Na Dalibai Dole Mu dinga Bibiyar Al’amuran Mu Tare da Magance Matsalolin Mu Dakan Mu.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Ka duba yanzu] Cut off Marks na jami’ar aikin soja dake garin Biu

Dole dalibi ya mallaki katin dan kasa kafin samun damar yin Jamb a shekara mai zuwa

BUK ta fitar da Cut off Marks ko akwai bukatar ka canja course din da ka nema?

Cut of Marks da hukumar Jamb ta amince dasu ga jami’o’i

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!