Cut of Marks da hukumar Jamb ta amince dasu ga jami’o’i

Home JAMB Cut of Marks da hukumar Jamb ta amince dasu ga jami’o’i
Cut of Marks da hukumar Jamb ta amince dasu ga jami’o’i

AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM

JAMB 2019 CUT OFF MARKS

Hukumar Jamb Ta fitar da Cut off Marks dinta ta Sanya 160 a matsayin mafi karancin Makin Shiga jami’oi’nmu!

Kamar yadda hukumar ta alkawarta yau ne zata saki cut off marks ta cika alkawari ta saki cut off marks din,

Saidai makin baiyi ma wasu mutane da yawa dadi ba kasancewar shekarar 2019 tana daya daga cikin shekaru wadanda dalibai suka koka abisa rashin samun sakamako mai kyau,

Cut of marks 160 yana nufin cewa babu wani dalibi dazae samu admission a jamiar Gwamnati Muddin Makinsa baikai 160 ba, duk da matsalar faduwar jarabawa da aka samu a bana.

Duk da kasancewar 160 yayi tsauri anawa ra’ayin amma wasu zasu ga kamar hakan zaesanya dalibai kara dagewa akan karatunsu kuma zae iya zama hanyar gyara Ilimi,

Nima a nawa bangaren banji dadin abubuwan da hukumar jamb tayi ba tun daga watan November da muka saka ran cewa zaa fara registration har zuwa yanzu data fidda mafi karancin makinta.

Gaskiya Banji dadin wannan hukunci ba kasancewar yan uwanmu dalibai dayawa baxasu samu damar shiga jamia ba,

Amma kuma wannan hukunci an yankeshi ne a gaban vice chancellors na jami’oinmu kuma basuce komai ba, amma naso ace ansaka 140 ko 150 a matsayin cut off marks din saboda dayawa daga cikin jami’oi suna kara nasu makin.

Duk da cewa Ministan Ilimi na kasa Malam Adamu Adamu bai halarci wurinba saedae wakilinsa,

Amma naso vice chancellors dinmu sun dage akan cewa a kara rageshi ya koma 150 ko 140 domin daliban arewa wadanda sune sukafi faduwa jarabawar su samu damar shiga jamia.

A karshe dae Ina fata da kuma adduan Allah yasa haka shine mafi alkhairi a gareku,

Sannan wannan zae zama Izina Agaremu da kuma kannenmu domin mu gyara mu tsaya muyi karatu domin mu yan Arewa mu aka Raina mu akeso aga an durkusar kuma Gashi Manyanmu sunyi shiru.

To Insha Allahu Mu Bazamuyi shiru ba Zamu fadi Gaskiya Komai Dacinta domin Cigaban Yankinmu.

A karshe Ina kara jawo hankalin Matasa da kuma Daliban Arewa akan Cewa mu kara kaimi wajen Kishin Kasa Musamman ma yankin mu na Arewa,

Asof kungiyace da aka kafa domin kare hakki na daliban Arewa dakuma haskaka masu hanyar dazasu bi domin kaiwa tudun muntsira.

Muhada Hannu da Asof domin mu magance matsalar kanmu da yan uwanmu.

Asof Tamuce Baki Daya.

 

Naku Abdulkadir Anas Malumfashi.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

Tallafin karatu ga daliban jihar Yobe masu 5 Credits

[School News] An fara sayar da form na School of basic Remedial Studies Funtua (ABU Zaria)

An Fara Sayar da Form Din Shiga Makarantar Shehu Sule College of Nursing and Midwifery Damaturu

An fara sayar da form na International University of Languages (iUOL)

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!