[Jamb] Yaushe Sakamakon Jamb Zai Fito? Dagaske ne Za’a Chanja Jarrabawar JAMB? – JAMB 2019

Home JAMB [Jamb] Yaushe Sakamakon Jamb Zai Fito? Dagaske ne Za’a Chanja Jarrabawar JAMB? – JAMB 2019
[Jamb] Yaushe Sakamakon Jamb Zai Fito? Dagaske ne Za’a Chanja Jarrabawar JAMB? – JAMB 2019

[Jamb] Yaushe Sakamakon Jamb Zai Fito? Dagaske ne Za’a Chanja Jarrabawar JAMB? – JAMB 2019

  • Dan Allah Yaushe Results Dinmu Zai Fito?
  • Results Din Mu Yazama inconclusive
  • 2019 ta kafa Tarihi a Hukumar JAMB
  • Kodai Macijiya Ce ta Hadiye Results Din?

 

Wadannan Sune irin Magan Ganun da Dalibai Sukeyi a Kan Sakamakon Jarrabawar Su ta JAMB, Wasu Sunayin Maganar Cikin Raha Wasu kuma Cikin Fusata.

Hakika Daliban Dasuka Rubuta Jarrabawar JAMB din ta 2019, Sun Shiga Dimuwa da Rashin Tabbas Tun bayan kwashe Kusan Sati Uku babu Labarin Results din Nasu, koda Yake Hukumar JAMB Tasha Nanata Cewa Tana Bincike ne Akan Sakamakon Jarrabawar Sbd Kaucewa Masu Aikata ba Dai Dai ba, Amman Abun Dubawa ko a Shekarar Data gabata Ma Hukumar tayi ikirarin Cewa ta Bibiyi Jarrabawar, ta Hanyar Amfani da CCTV CAMERAS Amman Ba’a Samu Wannan Jinkirin Ba.

Wani Abu Dayake ta Yawo Akan Sakamakon Jarrabawar JAMB din Shine Batun Cewa JAMB Zata Shirya Sabuwar Jarrabawa tare da Soke Wacce Akayi din, kwamitin Asof Na Quality Assurance Yasamu Wannan Tambayar So Shurin Masaki, Anyi ta Tambayar Shin Gaskiyane?

Tabbas ASOF Tayi Shiru Dafarko Domin kuwa bata Yada Duk wasu Bayanai Sai Tasamu Tabbacin Su, Akwai Bayanai Na Soke Jarrabawowin JAMB Din a Wasu Santocin Dakuma wasu Jahohin Amman Har yanzu Jamb din bata Kai ga Bayyana Su ba, Amman Maganar Cewa Za’a Chanja Jarrabawar Gaba Daya ba gaskiya Bace.

ASOF ta Tuntubi Hukumar JAMB Ta wasu Bangarorin Domin Samun ingancin Maganar, an Tabbatar Mana da Cewa Babu Maganar Soke Jarrabawar Duka tare da Shirya wata, Amman Dai Za’a Soke Duk wata Centre da Aka Sameta da karya Doka ko Satar Amsa.

Muna Fatan Samun Cikakkun Bayanai daga Hukumar ta JAMB a Ranar Litinin Me Zuwa.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Jamb] Abinda Yakamata Mu Sani Bayan Rubuta JAMB 001 -Asof

[Jamb] Ana Neman Zaluntar Iyaye Da Ƴaƴan Su –Na ‘Yar Talla

[Jamb] An Kammala Jarrabawar Jamb Ko Ina Sakamakon Ya Makale?

[Jamb] Ababe 12 Da Hukumar JAMB Ta Hana Shiga Dakin Jarrabawa Da Su

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!