[Jamb] Ana Neman Zaluntar Iyaye Da Ƴaƴan Su –Na ‘Yar Talla

Home JAMB [Jamb] Ana Neman Zaluntar Iyaye Da Ƴaƴan Su –Na ‘Yar Talla
[Jamb] Ana Neman Zaluntar Iyaye Da Ƴaƴan Su –Na ‘Yar Talla

[Jamb] Ana Neman Zaluntar Iyaye Da Ƴaƴan Su –Na ‘Yar Talla

 

Maganganu sun yawaita tun daga lokacin da aka fara gudanar da Jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakanni-in-dire wato Jamb har zuwa lokacin da aka kammala rubutata ana tsimayin sakamako. Kuma ba komai ya janyo maganganun ba sai yadda tun a lokacin da ake zanawa wasu ɗaliban basu ga sunayensu a cikin jerin waƴanda za su zana Jarrabawar ba, alhalin kuma suna riƙe da slip ɗin su da yake a matsayin shaidar sun siyi form ɗin jarabawar. Amma haka suna ji suna gani basu samu damar zanawa ba. Su kan su waƴanda suka samu damar zanawar har yanzu sakamakon su yaƙi fita, kuma har yanzu babu wata tartibiyar magana guda ɗaya daga bakin hukumar tsara jarabawar.

 

Tun bayan maƙalewar sakamakon aka samu labarin cewa sakamakon jarabawar ɗaliban nan ya salwanta sakamakon rikicewar na’urar dake ɗauke da wannan sakamako. Amma sai hukumar suka yi tsallen baɗake suka ƙaryata wannan batun. Bayan ƙaryatawar ma har da fito da batun wai za su binciki sakamakon jarabawoyin baya har na tsawon shekara 10 domin su tona asirin waƴanda suka saci amsa. Ba kuma dan komai suka fito da wannan batu ba sai dan su kawar da hankalin mutane akan gundarin abin da ake tsimayin suyi.

 

Ganin wannan yaudarar baza ta kai su ba shi ne suka sake bijiro da batun wai sun gano Ɗalibai kusan dubu 100 wai sun saci amsa. Sai nake ta mamakin ta wace hanya za su iya gano an saci amsa a jarabawar da a cikin na’ura mai ƙwaƙwalwa aka gudanar da ita? Kuma ta wace hanya za su iya gano wanda ya saci amsa a jarabawar da aka gudanar shekaru 10 baya da suka wuce? Ko da dai ban da ilimi a wannan fannin amma zahiriyyan nafi gano tsantsar rainin hankali da rainin wayo ga Ɗalibai da Iyayensu.

 

A yanzu ana ta yaɗa labarin cewa akwai yiwuwar Ɗalibai su sake dawowa su zana sabuwar jarabawa, dan gaskiyar zance sakamakon su ya salwanta. Amma hakan ma hukumar ta fito ta ƙaryata.

 

Idan har hakan ta kasance akwai ɗaliban da tafiya suka yo mai nisa domin su samu su zana wannan jarrabawa. Kuma ta yiwu a cikin su ɗin a samu waƴanda bashi iyayensu suka ciwo dan sa basu kuɗin mota da na abinci. Amma a haka a sake cewa sai sun sake ɗaukar nauyin waƴannan yaran nasu a karo na biyu saboda kuskuren wasu mutane marasa daraja da martaba.

 

Sun kasa fitowa su bayyanawa al’umma gaskiya akan wannan batun, amma tsabagen rainin hankali shi ne suke yunƙurin jirkitar da kuskuren nasu kan ɗaliban ta hanyar jifansu da satar amsa.

 

Duk waƴanda ya dace suyi magana akan wannan rashin sanin aikin na hukumar sunja baki sunyi shiru. Ko da yake al’amarin yafi shafar Ƴaƴan talakawa.

Wannan kuskuren kaɗai ya isa ya zame maka ƙarin hujja kan cewa wannan Gwabnatin bata da wani cikakken tsari na sanin makamar aiki, sai harigido da bankwara kawai.

 

Na Ƴar Talla
05-05-2019.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Jamb] An Kammala Jarrabawar Jamb Ko Ina Sakamakon Ya Makale?

[Jamb] Abinda Zakayi Idan Baka Ci Jamb ba, Abubuwan da zasu taimaka maka ka samu Admission a 2019

[Jamb] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 010-Asof

[Jamb 2019] Yadda Zaka Canja Jamb Dinka Zuwa D.E

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!