[Jamb] Abinda Yasa Bamu Saki Sakamakon Dalibai ba -Jamb

Home JAMB [Jamb] Abinda Yasa Bamu Saki Sakamakon Dalibai ba -Jamb
[Jamb] Abinda Yasa Bamu Saki Sakamakon Dalibai ba -Jamb

[Jamb] Abinda Yasa Bamu Saki Sakamakon Dalibai ba -Jamb

 

Hukumar Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB) Tayi bayani a daren talata akan dalilin da yasa har yanzu bata saki sakamakon jarabawar 2019 ba.

 

A yadda hukumar Jamb din tayi bayani Jinkirin da aka samu ya samo asaline saboda kokarin da hukumar take tayi wajan ganin Cewa ta hukunta dukkan wani mutum da aka samu da aikata laifin satar amsa a lokacin jarabawar a cikin Dalibai da kuma gwurbatattun maikatan da suka bawa dalibai satar Amsa, Jamb Tace ba zata bar wadannan masu laifi su tafi haka ba, ba tare da an hukunta su ba.

 

Sannan Hukumar JAMB din tayi karin bayani a shafinta naTwitter kamar haka:

“JAMB tana gargadin Jama’a Cewa hukumar har yanzu bata fitar da sakamakon jarabawar 2019 ba, kuma da zarar ta gama bankado wadanda suka aikata laifin satar amsa da bayar da amsoshi, toh zata saki sakamakon ba tare da ba tare da bata lokaci ba”.

 

“Kuma muna kara kira ga Dalibai cewa su tabbatar sun kara kulawa da profile codes dinsu da registration numbers dinsu. Saboda akwai wasu macuta da suke damfarar dalibai dasunan cewa su maikatan Jamb ne, a biyasu kudi su qara maka maki, toh kar ka sake ka basu wani bayani dangane da jarabawarka balle kuma kayi gigin basu kudinka, Yan Danfara ne”.

 

“Hukumar tace dukkan wani bayani dangane da jarabawar. Za’a saka shi a shafukan yana gizo na hukumar ne kadai wanda gashi nan a kasa kamar haka:

Jamb Board’s Official website

http://www.jamb.gov.ng

Mun san cewa dalibai sun Qosa suga sakamakonsu, Toh kar su damu muna gama fitar da wadannan masu laifi to JAMB zata turowa kowa da sakamakon shi ta email ko ta lambar wayar shi shi.

Marubuci: Ibrahim Assalafiy

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Jamb] Yaushe Sakamakon Jamb Zai Fito? Dagaske ne Za’a Chanja Jarrabawar JAMB? – JAMB 2019

[Jamb] Abinda Yakamata Mu Sani Bayan Rubuta JAMB 001 -Asof

[Jamb] Ana Neman Zaluntar Iyaye Da Ƴaƴan Su –Na ‘Yar Talla

[Jamb] An Kammala Jarrabawar Jamb Ko Ina Sakamakon Ya Makale?

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!