[Jamb] Abinda Yakamata Mu Sani Bayan Rubuta JAMB 001 -Asof

Home JAMB [Jamb] Abinda Yakamata Mu Sani Bayan Rubuta JAMB 001 -Asof
[Jamb] Abinda Yakamata Mu Sani Bayan Rubuta JAMB 001 -Asof

[Jamb] Abunda Yakamata Mu Sani Bayan Rubuta JAMB 001 -Asof

Kashi Na 1 (Cigaba)

(25-04-2019)

  • >Me Yakamata Nayi Bayan Nayi Jarrabawar JAMB?
  • >Me Yayi Saura?
  • >Shin Na jira Kawai Za’a Ban Admission?

Wani Lokacin Zumudin da Dalibi Yakeyi Na Rubuta JAMB Dinsa yana karewa ne da Zaran Sakamakon JAMB Yafito, ta Yuwu be Ci Makin Da yake So Yaci ba,

Shin Me Yakamata Nayi?

  • Wannan Tambayar Tana da Muhimman Ci Sosai.

Bayan Fitowar Sakamakon JAMB din ka Abubuwa Nafarko Dazaka Fara Dubawa Sune:

1•Maki Nawa kasamu?

2•Maki Nawa Jami’ar Daka Nema Take so ?

3•Maki Nawa Ake Nema a Departments din da Kake So?

4• Wanne Tsari Makarantar Daka Nema Takebi Wajen Bada Admission?

Idan Kuna Biye Damu a Darasin Mu Na baya Munyi Bayani Akan Abu Biyu Daga Cikin Hudun da Muka Lissafo a Sama, zamu Dora Daga inda Muka Tsaya.

 

  • Maki Nawa Ake Nema a Departments din da Kake So? Yana Daga Cikin Babbar Matsalar Da’ake Fuskanta, wani Lokacin Rashin Sanin Adadin Makin Din Da’ake Bukata, a Department din da Dalibi Yake Nema, Misali Kana Neman Computer Science a Federal University Dutsenma, Amman baka Sani ba ko Akwai wani Maki Na Musamman Da’aka Kebance dole Sai ka samu a Jamb Dinka kafin Abaka Admission din, wani Lokacin kuma Abun yana Komawa ne kan Combination Dinka Na SSCE idan akwai wani darasin da’ake Bukatar Dole Sai kaci.
  • >Yadda Za’a Magance Wannan Matsalar:

Na farko De Dole Dalibi Yazama yana Bibiyar Duk wasu Abubuwa Na Makarantar Da yake Nema Dakuma Department din, Sannan yana da kyau kasamu Wadan da Suke Wannan Department din Su dinga Fada Maka Abunda Yakamata Kayi, wani Lokacin kuma Sai kaje Wajen HOD din Da kanka Domin Samun Cikakken Bayani.

  • Wane Tsari Makarantar Daka Nema Takebi Wajen Bada Admission:

a Shekarar 2017 Wani Dalibi Ya Rubuta JAMB Yasamu Adadin Makin  Da ake Nema a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil Saidai Amma bayan Haka Baisan wani Abu da Zaiyi ba Anan Gaba, Yaje Gida Kawai yana jiran Admission bayan Lokaci Me Tsawo sai aka bukaci Zuwa Jami’ar Domin Tan-Tancewa Zuwan sa ke da Wuya Aka Tambaye Shi Slip Dinsa wanda yabiya Kudi kuma yayi online registration Amma kash!  Bai sani ba hakan tasa Ba’a Saurare Shi ba Yakoma gida.

Tabbas Dole ne Kasan irin Tsarin da Makarantar take bi shin Post-UTME takeyi kokuma Departmental Screening?

Da Zarar kaga Sakamakon JAMB din ka Yafito Kuma kasamu Makin Da ake Bukata, To daga Wannan Lokacin Zaka Fara Bibiyar Al’amuran Makarantar Sau da Kafa.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Jamb] Ana Neman Zaluntar Iyaye Da Ƴaƴan Su –Na ‘Yar Talla

[Jamb] An Kammala Jarrabawar Jamb Ko Ina Sakamakon Ya Makale?

[Jamb] Abinda Zakayi Idan Baka Ci Jamb ba, Abubuwan da zasu taimaka maka ka samu Admission a 2019

[Karanta Yanzu] Dalilin Da Yasa Dalibi Zaici Jamb Amman Ya Rasa Samun Admission

Zamu Cigaba insha Allah.

KARKU MANTA MATSALAR DALIBI DAYA MATSALAR MUCE DUKA KUZO MUHADU MU MAGANCE TA

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!