[Jamb] Abinda Zakayi Idan Baka Ci Jamb ba, Abubuwan da zasu taimaka maka ka samu Admission a 2019

Home Exam's [Jamb] Abinda Zakayi Idan Baka Ci Jamb ba, Abubuwan da zasu taimaka maka ka samu Admission a 2019
[Jamb] Abinda Zakayi Idan Baka Ci Jamb ba, Abubuwan da zasu taimaka maka ka samu Admission a 2019

[Jamb] Abinda Zakayi Idan Baka Ci Jamb ba, Abubuwan da zasu taimaka maka ka samu Admission a 2019

 

Idan baka samu makin da kake bukata ba Jamb kuma kana son ganin ka samu admission a 2019, rashin nasara a Jamb baya nuna cewa ba zaka samu admission ba don haka sai mutum ya canja hanya.

 

Zana Jarrabawar Jamb

Bayan ka zana Jamb sai baka samu 180 ko 200 ba, ba zuwa zakayi ka kashe kanka ba dan uwa, a matsayinka na musulmi daman dukkan al’amarinka kamata yayi ka mikashi ga Allah, sai kayi nazari shin wadannan matsaloli ka fuskanta wanda suka haifar da faduwarka, ina ne kake da matsala domin aga an gyarata.

 

Yayinda Ka Duba Sakamakon Jarrabawarka

A lokacin da ka samu sakon sakamakon jarrabawarka ko kuma kayi printing dinsa to ka fara tambayar kanka mutum nawa ne suka samu maki sama da kai? Mutum nawa ne suka samu maki wanda bai kai naka ba? Mutum nawa ne zasu samu admission a wannan shekarar daga cikin wadanda sukayi Jamb?

 

Daga nan sai ka duba sauran karatuka da akeyi kamar Pre-degree, Certificate, Basics, Remedial dasauransu, sai kayi kokarin neman domin magance matsalar zama haka.

 

Canja Course zuwa wanda ke kasa da wanda ka nema

Idan ka duba course din daka nema makinka bai kaishi ba to sai ka hanzarta zuwa neman na kasa dashi wanda ya dace da makin da ka samu.

 

Tsayawa cewa dole sai abinda kakeso zaka samu baya haifar da komai sai koma baya, wasu da dama sun shafe shekaru sama da biyar 5 suna zana Jamb amman basa yin nasara, sai ka tuno cewa mutum nawa ne suka nemi sabon darasin da zaka nema? Wato dai yin makarantar yafi zama haka, ta yaso shekara mai zuwa ka iya canjawa.

Allah ya bada sa’a.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Karanta Yanzu] Dalilin Da Yasa Dalibi Zaici Jamb Amman Ya Rasa Samun Admission

Yadda Zaka Samu Maki 270+ A Jamb

[Jamb] KARANTA YADDA ZA’A FARA JARRABAWAR JAMB

YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABAWAR JAMB

Basheer Sharfadi

08-04-2019.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!