[Jamb] Matsalar ThumbPrint a Jamb 2019

Home JAMB [Jamb] Matsalar ThumbPrint a Jamb 2019
[Jamb] Matsalar ThumbPrint a Jamb 2019

[Jamb] Matsalar ThumbPrint a Jamb 2019

 

DANGWALA YATSA (THUMBPRINT)

Tun da Farko De Hukumar ta JAMB ta bada Sanarwar Cewa Dukkan Daliban Dazasuyi Jarrabawar JAMB a Wannan Shekarar, idan sunada wani Rauni a Hannun Su ko wani Dalilin Dazaisa Na’urar Dangwala Hannun taki Daukar Hannun Su, to Sai De Suyi Rajistar JAMB Din a Babban Ofishin Su na Jamb Dake Abuja Hakama Jarrabawar Ma a Chan Zasuyi.

 

Amma ga Dalibin Dayayi Rajistar JAMB din kuma Hannun sa Yakarba a Lokacin Rajistar to idan a Lokacin Jarrabawar Hannun sa be Dauka ba to Shikenan bazeyi Jarrabawar ba Sam Sam, Kamar Yanda Hukumar ta Bayyana.

 

Da Wannan ne Kungira Dalibai ta Arewa Asof. Take Kara Jan Hankalin Al’umma Musamman Mata da Kada Suyi Lalle/Kunshi, har sai bayan kammala Jarrabawar.

 

Haka Ma Mazan Musamman Wanda Ayyukan su suka Shafi Yin Aiki da Hannu Kamar Ayyukan Gona da Makaman tan Su Yakamata Su kiyaye Har bayan kammala Jarrabawar.

 

Thumbprint ko Dangwala Hannu Abune da Kowanne Dalibin da Yayi Rajistar ta JAMB Yayishi a Lokacin Yin Rajistar.

Kamar Yanda Kowanne Dalibi ya Dangwala Hannun sa a Na’urar Dangwala, Hannu Lokacin Rajistar ta JAMB Hakama Lokacin dazeyi Jarrabawar sai ya kara Dangwala Hannun sa Hakama bayan Gama Jarrabawar.

Ka Kula Sosai da Cewa Sai ka Dangwala Hannun ka bayan kagama Dakuma kafin Fara Jarrabawar, Rashin Yin Hakan Na iya Haifar Maka da Matsala, ta absent, Wato Ace Sam Bakayi Jarrabawar JAMB din ba.

 

Hukumar ta JAMB tayi Gargadin Cewa Duk Wanda Hannun sa Bekarbi Naurar Dangwala Hannun ba, to bazeyi Jarrabawar ba.

 

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Jamb 2019] Thumbprint Dolene ga Dalibi Kafin Zana Jarrabawa –Inji Hukumar Jamb

[Jamb] Me ake Nufi da Jarabawar Mock (Mock Examination) da Abubuwan da ta Kunsa?

[Jamb 2019] Yadda Zaka Canja Jamb Dinka Zuwa D.E

[Karanta Yanzu] Matsalolin Da Ake Fuskanta Wajen Yin Register Jamb

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!