[Jamb] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 005

Home JAMB [Jamb] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 005
[Jamb] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 005

[Jamb] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 005

 

(15-03-2019)

Shin Ban iya Computer Bane?

Shin Ban iya Karatun Bane?

Mecece Matsalar?

 

Karanta Rubutuka da Suka Gabata:

Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB? 001 -Arewa Asof

Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB? 002 -Arewa Asof

[Jamb] Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB Kashi na 003? -Arewa ASOF

 

Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka.

Kungiyar Asof. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa Jarrabawar JAMB,

Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar JAMB so Biyu wasu So Uku wani Ma da Asof. Ta Tattauna Dashi So biyar Yayi JAMB beci Ba!

 

A ina Matsalar Take?

Matsala Ta Takwas

Tilastawa Dalibi Yacike Abinda Bashi Yakesoba: –

Wannan matsalace data zama ruwan dare, domin kuwa a halin yanzu mafiya yawan iyaye sunada wannan dabi’ar ta tilastawa Dalibi yacike abinda su sukeso koda kuwa shi dannasu ba wannan abin yakesoba, su babu ruwansu

Wanda hakan ba daidaibane domin kuwa yakan iya saka Dalibin a hali na damuwa, da kuma rashin sha’awar yin karatu, wanda zai iya jawo masa matsalar faduwa wannan jarrabawar ta jamb.

Dalilin dayasa kuwa dalibai suke bijirewa dabi’ar yin karatun shine, saboda suna ganin cewa tunda aka hanasu, su cike abinda sukeso alokacin rijistar jamb din to kuwa suma bazasuyi karatunba, da zummar ramuwar gayya

Kaina takaice mukuma wasu daliban ko meaning daya basa karantawa, da zummar wai suci jamb, idan akayi musu irin haka.

 

Shawarwari Akan Wannan Matsalar: –

  • Yanada kyau iyaye subar ‘ya’yansu su zabi abinda sukeso, saboda kowa akwai yadda ya tsara rayuwarsa tanan gaba.
  • Yanada kyau ‘ya’ya sudinga daukar matakin wayar dakan iyayensu akan amfanin barin yaro yazabi career dinsa tanan gaba.
  • To kamar yadda ‘ya’ya zasu dauki matakin wayar dakan iyayensu, to hakama yanada kyau kungiyoyi su taimaka fagen yin wannan aikin.

 

Matsala Ta Tara

 

Yin Amfani da Social Media (Shafukan Sada Zumunta) Da Kuma Wasu Abubuwa Masu Daukar Hankali Fiyeda Kima: –

A halin yanzu mafiya yawan dalibai sun lalace, abinda nake nufi dasun lalace kuwa shine sunayin amfani da abubuwa masu shagaltarwa, fiyeda kima,

A halin damuke ciki yanzu zaka iya ganin dalibi, yayi samada awa 5 yana chatting ko kuma wani abu mai shagaltarwa wanda wannan ba daidaibane.

Dalibi katuna wannanfa shine lokacinka na karatu daga yawuce, to kuwa babu kai babu samun damar yin karatu, saboda nan gaba koda kayima bazai zaunaba.

 

Shawarwari Akan Wannan Matsalar: –

  1. Yana Da kyau musani cewa yanzufa shine lokacinmu na karatu, saboda haka baikamata mubatashi da sharholiyar duniyaba
  2. Wannan chatting din da game lokacinsu baya kurewa kabari kayi nan gaba, amma kuwa shi karatu lokacinsa yana kurewa
  3. Bawai kar ayi amfani da social mediaba, a’a shima social media yanada nasa amfanin, amma mudingayin amfani dashi daidai
  4. Yanada kyau musani cewa jarrabawar nan fa ta jamb ta karato, saboda haka yanzu yakamata muyi amfani da wadannan shawarwarin.

DAGA TASKAR ASOF.

Mai Rubutu: – Miftahu Ahmad Panda.

(Mataimaki Na Musamman ga Secratery General Na Asof.)

Zamuci Gaba insha Allah.

 

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Jamb] An Sanya Ranar Fara Cirar e-Slip da Kuma Ranar Fara Jarrabawar Jamb

[Jamb] Me ake Nufi da Jarabawar Mock (Mock Examination) da Abubuwan da ta Kunsa?

[Jamb 2019] Thumbprint Dolene ga Dalibi Kafin Zana Jarrabawa –Inji Hukumar Jamb

[[Jamb 2019]] Tambaya da Amsa daga Littafin Sweet Sixteen cikin harshen Hausa

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!