[Jamb] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 004

Home JAMB [Jamb] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 004
[Jamb] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 004

[Jamb] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 004

 

(08-03-2019)

Shin Ban iya Computer Bane?

Shin Ban iya Karatun Bane?

Mecece Matsalar?

Karanta Rubutuka da Suka Gabata:

Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB? 001 -Arewa Asof

Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB? 002 -Arewa Asof

[Jamb] Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB Kashi na 003? -Arewa ASOF

 

Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka.

 

Kungiyar Asof. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa Jarrabawar JAMB,

Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar JAMB so Biyu wasu So Uku wani Ma da Asof. Ta Tattauna Dashi So biyar Yayi JAMB beci Ba!

A ina Matsalar Take?

Matsala Ta Shida

  • Rashin iya managing din time (Rashin iya lura da lokaci): –

A lokuta dayawa Dalibai sunayin karatu yanda yakamata, kuma abinda suka karanta yana fitowa a cikin wannan jarrabawa, amman saidai kash!!! lokaci yana samar musu da matsala, saboda basu da saurin da zasu iya kammala amsa tambayoyin nasu a lokacin da hukumar ta kayyade na awa 2.

Hakanne yasa suke rasa maki maiyawa, daga karshe kaga sun fadi wannan jarrabawa.

To ammafa dalibai kada kutsorata, domin bawai lokacin ne yakeyin kadan ba, awa 2 zata isheka/isheki kugama amsa tambayoyinku guda 180 harma kayi ragowa, matukar zakabi lokacin naka yadda yakamata, ma’ana basai kayi saurin daya wuce kimaba kuma karka tsaya wasa(lala) har lokacin naka yakare.

Mafita akan wannan matsalar: –

1- Dalibi yatabbatar dacewa ya amsa tambayoyinsa cikin sassarfa ma’ana basauri sosaiba kuma ba lalaba.

2- Dalibi yatabbatar dacewa yana lura da lokacinsa alokacin dayake amsa jarrabawar.

3- Dazarar dalibi yaga cewa lokacinsa yarage kadan misali seconds 20, to yayi submitting duk da cewa jamb ta tsara abin akan cewa lokacinka yana cika computer zata dauke tayi submitting dakanta to amma wasu lokutan akan iya samun matsala.

 

Matsala Ta Bakwai

 

  • Rashin Yin Addu’a: –

Duk da dai nasan cewa dalibai dayawa zasuce meya kawo wannan a cikin dalilan faduwa jamb?to kuwa akwai dalili:-

Domin babu addinin da bai yarda da addu’a ba, either musulinci ko kiristanci.

Hakika Jarrabawa mai hadari irin jamb tana bukatar addu’a fiyeda kowacce jarrabawa.

Kuma addu’ar bawai taka kai kadaiba, A’a wannan addu’ar ta hada da addu’ar iyaye, yayyu,kannu dadai sauran dangi, saboda addu’arka kai kadai aganina bazata wadatarba dole sai an hada data walidai.

  • Shawarwari Akan Wannan Matsalar: –
  • Dalibi yatabbatar dacewa yayi addu’a kafin dakuma bayan yin jarrabawarsa
  • Sannan yatabbatar addu’ar iyayensa tashigo ciki, domin addu’arsu karbabbiyace, musammanma ta uwa
  • Sannan da addu’ar kannai,yayyu dadai sauran dangi baki daya
  • Ina ganinma idan Allah yahorewa dalibi yadingayin sadaka, tareda sanar da masallatan unguwarsu cewa a tayashi da addu’a akan wannan bukata tasa.

 

By: – Miftahu Ahmad Panda (Special Assistant to Secretary General of Asof).

 

DAGA TASKAR ASOF.

Zamuci Gaba insha Allah.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Jamb] An Sanya Ranar Fara Cirar e-Slip da Kuma Ranar Fara Jarrabawar Jamb

[Jamb] Me ake Nufi da Jarabawar Mock (Mock Examination) da Abubuwan da ta Kunsa?

[Jamb 2019] Thumbprint Dolene ga Dalibi Kafin Zana Jarrabawa –Inji Hukumar Jamb

[[Jamb 2019]] Tambaya da Amsa daga Littafin Sweet Sixteen cikin harshen Hausa

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!