[Jamb] An Sanya Ranar Fara Cirar e-Slip da Kuma Ranar Fara Jarrabawar Jamb

Home JAMB [Jamb] An Sanya Ranar Fara Cirar e-Slip da Kuma Ranar Fara Jarrabawar Jamb
[Jamb] An Sanya Ranar Fara Cirar e-Slip da Kuma Ranar Fara Jarrabawar Jamb

[Jamb] An Sanya Ranar Fara Cirar e-Slip da Kuma Ranar Fara Jarrabawar Jamb

 

Hukumar Shirya Jarabawar Share fagen shiga Jami’a wato Jamb ta sanya ranar 1th ga watan April a matsayin ranar da za’a gudanar da Jarabawar Mock a duk fadin kasar, hakan yazo ne sakamakon Zabukan da basu kammalu ba wanda za’a karasa a wasu Jihohin kasar nan ranar 23, ga watan March wadda tayi daidai da ranar da za’a gudanar da Jarabawar Mock din kamar yadda Hukumar ta Jamb ta sanya tun da farko, Saidai Canja zaben a wasu Jihohin ya tilastawa Hukumar ta Jamb dage ranar yin Mock din daga 23rd March zuwa 1st April, 2019.

Saboda haka yanzu Jarabawar Mock za’a yita ne a ranar 1st April 2019.

A wani bangaren kuma hukumar Jamb tana kara sanar da dalibai cewa duk wanda ya riga yayi Printing na Mock Examination Slip dinsa to ba sai ya kara yin wani Printing din ba, Saboda babu wani abunda aka canja illa kawai ranar da za’ayi Mock din.

Haka kuma Hukumar ta Jamb ta sanya ranar 2nd, ga watan April din a matsayin ranar da za’a fara Printing na Slip din Jarabawar ta Jamb, don haka take jan kunnen kowanne dalibi da ya tabbatar yayi Printing Din Jamb Examination Slip din nasa kafin ranar da zaiyi Jarabawar.

Kuma kowanne dalibi zai iya yin Printing din Slip din nashi a ko ina ne ba dole sai a CBT centre ba.

Hakanan Hukumar ta bayyana ranar 11, ga watan April matsayin ranar ne za’a fara gudanar da babbar Jarabawar ta Jamb wacce za’a share har tsawon sati guda anayi.

Allah Ya Bada Sa’a Amin.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[[Jamb 2019]] Tambaya da Amsa daga Littafin Sweet Sixteen cikin harshen Hausa

YADDA AKE CIRAR SLIP DIN JAMB NA WANNAN SHEKARAR 2019

Yadda Zaka Samu Maki 270+ A Jamb

[Jamb] Me ake Nufi da Jarabawar Mock (Mock Examination) da Abubuwan da ta Kunsa?

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!