[Mu San Makarantunmu] Government Secondary School Panda, Gaya Zone, Kano

Home Secondary School [Mu San Makarantunmu] Government Secondary School Panda, Gaya Zone, Kano
[Mu San Makarantunmu] Government Secondary School Panda, Gaya Zone, Kano

[Mu San Makarantunmu] Government Secondary School Panda, Gaya Zone, Kano

 

Wannan Wani Program Ne Da kungiyar dalibai ta Arewa Asof. Ta Kirkiro Domin Fahimtar Halin da Makarantun Mu Na Sikandire Suke Ciki Musamman Na Yankunan Dasuke Kauyuka da Karkara.

Wannan Lokacin Mun Samu Tattauna Wa da Wani Matashin Dalibi Dan Aji Ukun karshe a Sikandiren Cikin Garin Panda. (Miftahu Ahmad Panda)

 

Government Secondary School Panda: –

An kirkiri wannan makaranta maisuna asama, a shekarar 1987, a Matsayin Junior Secondary School, idan mutum yayi BECE ma’ana jarrabawar kammala karamar secondary wanda dalibai sukafi sani da PLACEMENT, to saidai yatafi wata makarantar yayi karatunsa Senior Secondary School.

A shekarar 2008, Allah yasa gwamnatin jihar kano, karkashin jagorancin gwamnan jihar kano na wancan lokacin Mallam Ibrahim Shekarau ta mayar da ita babbar secondary bisa jajircewar principal din makarantar na wancan lokacin maisuna Malam Abdussalam wanda akafi sani da SHAGOGO, Allah yayi masa rasuwa a shekarar 2018, Muna fatan Allah yayi masa rahama.

Yawan Daliban Makarantar: –

G.S.S. Panda tanada dalibai akalla guda dari shida(600, Saidai wasu daga cikin daliban suna fashi musamman ma wadanda suke a babbar secondary(Senior)wanda yakama daga S.S.1 zuwa S.S.3, amma duk da hakan anasamun dalibai da Dama Suna Halartar Makaranta

“hakan kuwa yafarune bisa kammala jarrabawar QUALIFYING damukayi, kuma haryanzu sakamako baifitoba, shiyasa wasu daga cikinsu suka tafi garurruka kamar: – Abuja, Lagos dasauransu da zummar neman kudi” -Miftahu Ahmad Panda (Dalibin ss3 a Makarantar)

A bangaren junior kuwa suna zuwa makaranta yadda yakamata babu fashi ballantana makara. wannan shine takaitaccen bayani akan yawan daliban g.s.s. panda dakuma yadda suke zuwa makaranta.

Malaman Makarantar: –

A bangaren yawan malamai zan iya cewa G.S.S. PANDA makarantace da bayabo bafallasa, domin tanada malamai akalla guda ashirin wanda suke koyarda darussa daban-daban.

“saidai duk da hakan G.S.S. Panda tanada matsalar malamai na darussa guda biyu  yanzu haka, junior munada matsalar malamin physical and health educationp.h.e), yayinda senior kuma mukeda matsalar malamin physics”

Principal: Principal Malam Sule Abdu.

Vice principal: Malam Sabi’u Shehu

Senior master: Malam Sunusi Abubakar

Examination officer: Malam Abubakar Muhammad. Da sauransu.

Haka kuma Makarantar Tana da Malaman Sa Kai (Volunteer) Dakuma Malamai Yan Bautar kasa (NYSC).

Ajujuwan Makarantar: –

G.S.S. Panda tana da blocks guda bakwai, a yayinda kowanne block yake daukeda ajujuwa guda biyu, Sannan Akwai SCIENCE LABORATORY Sai LIBRARY.

Darussan Da’akeyi a Junior: –

1- English Language

2- Mathematics

3- Computer Studies

4- Cultural and Creative Art

5- Civic Education

6- Security Education

7- Agricultural Science

8- Hausa

9- Islamic Studies

10- Social Studies

11- Basic Science

Sai kuma na goma shabiyu wanda shine babu malaminsa wato Physical And Health Education (P.H.E).

A senior darussan da akeyi sun kasu zuwa bangare biyu SCIENCE dakuma ART. bari mufara da Science.

SCIENCE: –

1- English Language

2- Mathematics

3- Chemistry

4- Biology

5- PhysicsAmma Bamuda Permanent Malami Saidai Masu Zuwa Suna Taimakawa).

6- Animal Husbandry

7- Civic Education

8- Islamic Studies

9- Computer Studies.

ARTSocial Sciences): –

1- English Language

2- Mathematics

3- Economics

4- Geography

5- Animal Husbandry

6- Islamic Studies

7- Computer Studies

8- Civic Education

9- Biology.

Wadannan sune darussan da akeyi a wannan makaranta mai albarka ta G.S.S. PANDA.

Kokarin Malamanta: –

A zahirin gaskiya malaman wannan makaranta sunayin iya bakin kokarinsu wajen ganin sun ciyar da wannan makaranta gaba ta hanyar zuwa su koyarda darussansu kamar yadda ya kamata.

A kwanannanma aka aikowa daya daga cikin malaman namu takardar jinjina da godiya daga zone din da makarantar take ma’ana GAYA, bisa jajircewarsa akan aikinsa, tareda umartarsa akan cewar yasake zage dantse.

Sannan bisa jajircewar Principal din wannan makaranta na baya dayawuce ansamar mana da ayyuka da dama, daga ciki akwai:-

1- Samo Mana Ginin Block Mai Dauke Da Ajujuwa Guda Uku

2- Gyaran Wani Aji

3- Fente Allunan Makarantar

4- Gyara Corpers Lodge Yimasa Fenti

5- Nemo Karin Malamai, da sauransu.

G.S.S. Panda makarantace da Allah yayiwa baiwar cin jarrabawar NECO, domin kuwa a iya sanina ban tabajin wata shekara da akace anfadi NECO a makarantarba, hakanne ma yasa take samun dalibai EXTERNAL da dama dasuke zuwa suke zana wannan jarrabawa.

 

Kar Ku Manta Kuma Zaku iya Turo Mana da Bayanan Makarantun Sakandiren Ku Domin Tan-Tancewa Dakuma Nazari Akai

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Jamb 2019] Yadda Zaka Canja Jamb Dinka Zuwa D.E

Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB? 002 -Arewa Asof

[Karanta Yanzu] Matsalolin Da Ake Fuskanta Wajen Yin Register Jamb

[Karanta Yanzu] Menene Ban-bancin UTME, JAMB, da Post UTME?

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!