[Jamb] Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB Kashi na 003? -Arewa ASOF

Home JAMB [Jamb] Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB Kashi na 003? -Arewa ASOF
[Jamb] Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB Kashi na 003? -Arewa ASOF

[Jamb] Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB Kashi na 003? -Arewa ASOF

 

KARANTA RUBUTUKAN DA SUKA GABATA:

Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB? 001 -Arewa Asof

Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB? 002 -Arewa Asof

 • Shin Ban iya Computer Bane?
 • Shin Ban iya Karatun Bane?
 • Mecece Matsalar?

Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka.

Kungiyar ASOF. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa Jarrabawar JAMB,

Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar JAMB sau Biyu wasu Sau Uku wani Ma da ASOF. Ta Tattauna Dashi Sau biyar Yayi JAMB baici ba!

A ina Matsalar Take?

Matsala Ta Hudu

 • Rashin samun Good Background (Tushe maikyau): –

Sanin kowane ba’ayin gini saida saida foundation, to a bangaren ilimima haka abin yake, matukar dalibi baifito daga makarantar da’akeyin karatuba to kuwa bazaiyi karatuba, domin hausawa suna cewa ice tun yana danye ake malkwasashi idan yabushe saidai yakarye, matukar dalibi yafito daga makarantar da ba’a karatu tozai dauka ko inama haka yake, saboda haka zai dauka cin jarrabawama basai anyi karatuba, hakan kuwa zai sakashi yasakankance akan hakan daga bisani kuma idan yayi jarrabawar jamb yafadi, to ananne zai gane cewa tunaninsa bamai kyaubane.

MAFITA: –

 • Yanada kyau iyaye su fahimci makarantun daya dace sukai ‘ya’yansu, ma’ana makarantun da’aka tabbatar cewa suna karatu yadda yakamata.
 • Sannan ga daliban da aka bawa mulki a makarantun secondary su tabbatar dacewa dadin mulki bai dauke musu hankali yahanasu karatuba.
 • Sannan koda iyaye basu fahimci cewa makarantarku ba’a karatuba, kayi/kiyi kokari kisanar dasu da zarar kin fuskanci hakan domin adauki mataki.

 

Matsala Ta Biyar: –

 • Yarda/Dogara da wasu wadanda suke kiran kansu exam helpers: –

A zahirin gaskiya wannan matsalace data zama ruwan dare game duniya, domin kuwa a halin yanzu akwai wasu mutane dasuke karbar kudade a hannun dalibai dasunan exam helpers, wanda hakan yana haifar da matsaloli ga daliban dasuka yarda suka bada kudinsu da sunan za’a taimaka musu suci jarrabawa, kaini naga wanima wanda yake cewa dalibai basai sunyi karatuba suna zuwa kawai zasuga an amsa musu jarrabawar saidai suyi submitting

Wannan kuwa ba karamar matsalabace, domin babu wanda ya isa ya hau system din jamb harya amsa maka tambayoyi.

Wasu kuma suna cewa zasu turo maka amsar jarrabawar, ana saura awa 2 ko 3 ka shiga/ki shiga wannan jarrabawa, wanda wannan duk ba gaskiya bane.

 • Shawarwari Akan Wannan Matsalar: –
 • Kada kayarda wani mutum yakarbi kudinka dasunan exam helpers
 • Sannan kada ka fadawa wani registration numberka ko profile password dinka, saboda dashi suke amfani su shirya amsoshinsu na karya, suce wai questions dinkane sukarbi kudi a gurinka
 • Kuma dan Allah wadanda sukeyin wannan hali su bari domin acikinmu suke
 • Yakamata hukumar jamb tadinga daukar mataki akan duk wanda aka kama yana karbar kudade a hannun dalibai da sunan zai taimaka musu a jarrabawa.

 

Marubuci: Miftahu Ahmad Panda. (Special Assistant to Secratery General)

Zamuci Gaba insha Allah.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Jamb 2019] Yadda Zaka Canja Jamb Dinka Zuwa D.E

[Jamb 2019] Bayan Kammala Register Ko Yaushe Za’a Fara Cirar Jamb e-Slip?

[[Jamb 2019]] Tambaya da Amsa daga Littafin Sweet Sixteen cikin harshen Hausa

Littafi Kyauta Ga Daliban da Zasu Zana Jarrabawar Jamb 2019

[Karanta Yanzu] Menene Ban-bancin UTME, JAMB, da Post UTME?

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!