[Jamb] Me ake Nufi da Jarabawar Mock (Mock Examination) da Abubuwan da ta Kunsa?

Home JAMB [Jamb] Me ake Nufi da Jarabawar Mock (Mock Examination) da Abubuwan da ta Kunsa?
[Jamb] Me ake Nufi da Jarabawar Mock (Mock Examination) da Abubuwan da ta Kunsa?

[Jamb] Me ake Nufi da Jarabawar Mock (Mock Examination) da Abubuwan da ta Kunsa?

Mock Examination wata Jarabawa ce da ake yi ta gwaji ga daliban da zasu zana jarrabawar Jamb, amma ba’a amfani da Makin da mutum ya samu a Jarabawar. Kawai ana yin ta ne don dalibi ya samu kwarewa a Jarabawa ta gaba da zaiyi.

KARANTA:- Mecece Jarrabawar Jamb? Da Kuma Tarihinta

Hukumar Shirya Jarabawar Share fagen shiga Jami’a (Jamb) ta fara Shirya Jarabawar Mock a Shekarar 2017. Hukumar ta nuna matukar damuwar ta akan yadda dalibai suke faduwa Jarabawar ta jamb bawai dan ba suda karatun ba ko kuma dan basu sani ba, a’a sai dai dan kawai basu san yadda Computer din take aiki ba, hasalima wasu basu taba danna Computer ba kuma sai gashi ance yau da ita zasuyi Jarabawa, kunga dole a samu matsala, dan haka ne Hukumar ta samar da ko ta kirkiri wannan Jarabawar ta Mock. Inji Dr. Benjamin.

 

Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Gameda Jarabawar Mock: –

  1. Ita wannan Jarabawar ta Mock ba dole bane sai kayi, idan kaga kanaso, zaka iya yi, idan kuma bakaso to daman ba dole bane. Kawai daman ana yinta ne don dalibi ya samu gogewa akan yadda akeyin Jarabawar
  2. Haka kuma duk makin da ka samu a Mock baza’a karashi acikin makinka na Jarabawar jamb ba, haka ma idan faduwa kayi to shima bazai shafi Jamb dinka ba, Saboda ba suda alaka da juna.
  3. Hakanan kuma babu abinda zai faru idan ka cika cewa zakayi Jarabawar ta Mock sai kuma ya zama baka samu yi ba, ko da kuwa da gangan kaki yi.
  4. Sannan tambayoyin da ka gani a Mock din ba wai lallai sune kokuma irin su ne za’a tambayeka a jamb ba.
  5. Sannan idan zakaje yin Mock Examination din to ka tabbata ka tafi da Slip dinka wanda kayi Printing na Mock Examination din
  6. Akarshe karkaje dakin Jarabawar ta Mock da duk wani abu da kasan Hukumar ta Jamb ta Haramta Shiga dashi dakin Jarabawar

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[[Jamb 2019]] Tambaya da Amsa daga Littafin Sweet Sixteen cikin harshen Hausa

Littafi Kyauta Ga Daliban da Zasu Zana Jarrabawar Jamb 2019

[Kayi Download Yanzu] Syllabus Na Jamb 2019

[Karanta Yanzu] Abubuwan Da Yakamata Ka Sani Kafin Kayi Register Jamb 2019

[Karanta Yanzu] Menene Ban-bancin UTME, JAMB, da Post UTME?

Yadda Zaka Samu Maki 270+ A Jamb

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!