[Jamb 2019] Thumbprint Dolene ga Dalibi Kafin Zana Jarrabawa –Inji Hukumar Jamb

Home JAMB [Jamb 2019] Thumbprint Dolene ga Dalibi Kafin Zana Jarrabawa –Inji Hukumar Jamb
[Jamb 2019] Thumbprint Dolene ga Dalibi Kafin Zana Jarrabawa –Inji Hukumar Jamb

[Jamb 2019] Thumbprint Dolene ga Dalibi Kafin Zana Jarrabawa –Inji Hukumar Jamb

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami’a wato Jamb a takardar bayanai da take fitarwa mako-mako a birin Lagos ta bayyana cewa tilas ne tayi amfani da na’ura tantance bayanan dalibai wato Biometrics Verification Machine (BVM) a turance, domin tantance daliban da zasu zana jarrabawar.

 

Tun a yayin register jarrabawar dai dalibai kanyi dangwalen hannu wato thumbprint wanda shine na’ura ke amfani dashi, haka kuma idan dalibi yaje zana jarrabawar to zai karayi domin tabbatar da cewa shine, sai dai dangwalen na baiwa wasu daga dalibai matsala, amman duk da haka hukumar jamb ta bayyana cewa ya zamo mata tilas ne yin amfani da wannan hanya da kuma wannan na’ura wajen tantance daliban domin magance matsalar satar jarrabawa.

 

“Babban dalilin da yasa tilas muyi amfani da wannan hanya shine saboda dalilai na tabbatar da tsaro, da kuma bada kariya ta yadda babu wanda zai iya zanawa wani jarrabawar, wato babu wanda zai hau sunan wani, mun dauki dukkan ‘yan yatsu guda goma na daliban, kuma dashi zamu tantancesu don su samu shiga dakin jarrabawa”

 

“akwai hanyoyin tantancewa da yawa, amman jamb ta zabi wannan hanyar ta dangwale saboda kaucewa samun matsalolin da ka iya zuwa, sannan babu dalibin da zamu bari ya zauna a dakin jarrabawa matukar baiyi wannan tantancewa ba”

 

A bangaren daliban da suka samu matsalar thumbprint din kuwa jamb ta bayyana cewa: “duk dalibin da yake da matsala dangane dayin thumbprint to ya gaggauta ziyartar babban ofishin hukumar dake birnin tarayya Abuja”

 

An samu dalibai guda 52 wadanda suka samu wannan matsalar a bana kuma 22 sun isa babban ofishin hukumar dake birnin tarayya Abuja.

 

A wannan shekarar dai dalibai sama da Miliyan Daya da Dubu Dari Takwas 1.8M ne sukayi register jarrabawar kamar yadda hukumar ta bayyana.

 

Allah ya kyauta, ya bada s’a amin.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

[Jamb 2019] Yadda Zaka Canja Jamb Dinka Zuwa D.E

[Jamb 2019] Bayan Kammala Register Ko Yaushe Za’a Fara Cirar Jamb e-Slip?

[[Jamb 2019]] Tambaya da Amsa daga Littafin Sweet Sixteen cikin harshen Hausa

Meyasa Na Fadi Jarrabawar JAMB? 002 -Arewa Asof

[Karanta Yanzu] Dalilin Da Yasa Dalibi Zaici Jamb Amman Ya Rasa Samun Admission

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!