[Jamb 2019] Yadda Zaka Canja Jamb Dinka Zuwa D.E

Home Exam's [Jamb 2019] Yadda Zaka Canja Jamb Dinka Zuwa D.E
[Jamb 2019] Yadda Zaka Canja Jamb Dinka Zuwa D.E

[Jamb 2019] Yadda Zaka Canja Jamb Dinka Zuwa DE

Ko Kasan zaka iya yin Upgrading (Converting) din Jamb dinka zuwa D.E ?

Hukumar Shirya Jarabawar Share fagen shiga Jami’a ta Kasa (Jamb) a kakar karatu ta Shekarar 2019/2020 ta fitar da wani tsari mai ban sha’awa wanda a Shekarun baya babu irin shi.

Kamar Yadda kowa ya sani ana samun kuskure wajen Siyan E-pin na jamb, wanda zakuga madadin a siya maka na D.E sai a kuskure a siya maka na jamb, to a wannan Shekarar Hukumar tayi kokarin ganin ta magance wannan matsalar ta hanyar bawa dalibai damar mayar da Jamb din su zuwa D.E ba tare da wani chaji ba (na kudi).

Don haka idan har ka samu irin wannan matsalar to ka kwantar da hankalin ka yanzu zaka iya canja ko mayar da Jamb din naka zuwa D.E.

A wani karin cigaban kuma Misali idan kayi Jamb kaga bakaci ba, to kuma kanada requirements (ka cika sharuda) na D.E shima zaka iya canja jamb din zuwa D.E, Ko kuma idan ya kasance lokacin da ka siya Jamb dinka baka da requirements na D.E sai daga baya ka samu, shima zaka iya canja jamb din zuwa D.E.

YADDA AKE CANJAWA:

Ga duk mai bukatar canja Jamb zuwa D.E sai ka ziyarci Ofishin hukumar Jamb na jiharka, ko kuma cibiyoyin da Jamb ta amince dasu.

Allah ya bada Sa’a

 

RUBUTUKA MASU ALAKA:
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!