[Jamb] Tambaya da Amsa daga Littafin Sweet Sixteen cikin harshen Hausa

[Jamb] Tambaya da Amsa daga Littafin Sweet Sixteen cikin harshen Hausa

Kamar kowace shekarar, Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a wato Jamb ta sanya littafin SWEET SIXTEEN wallafar BOLAJI ABDULLAHI a matsayin littafin da dalibai zasu karanta wanda acikinsa ne JAMB zata tsarma musu tambayoyin yaren Turanci.

Mun zakulo muku wasu tambayoyi da zasu iya kasancewa cikin tambayoyin da zasu zo daga littafin, mun kuma kawo muku su da amsoshinsu cikin harshen Hausa domin ku dalibai

Rubutuka Masu Alaka:

Yadda Zaka Samu Maki 270 zuwa sama a Jamb

Abubuwan da Yakamata Ka Sani Kafin Register Jamb 2019

Wacece Aliya?

Aliya itace jigon labarin littafin Sweet Sixteen, ita kadaice a wurin iyayenta, tana samun kulawa sosai, tana da kusanci sosai da mahaifinta, sai dai tana fuskantar wasu kalubale a makaranta.

Waye Mr. Bello?

Mr. Bello shine mahaifin Aliya, Dan Jarida ne, yana bala’in sonta sosai, don haka ya zuba idanunsa akanta qwarai da gaske.

Wacece Mrs. Bello?

Mrs. Bello itace Mahaifiyar Aliya matar Mr. Bello.

Wacece Big Mummy?

Big Mummy itace kakar Aliya, Mahaifiyar Mr. Bello, Surukar Mrs. Bello Kenan.

Wacece Aunty Molara?

Aunty Molara kanwar Mrs, Bello ce mahaifiyar Aliya, Kenan ita kanwar babar Aliya ce (Aunty).

Wanene Principal?

Tsoho ne sosai idan muka kwatantashi da Mr. Bello baban Aliya, amman ya zama aboki sosai a wurin baban Aliyan, Principal Christa ne dan kabilar TIV.

Wanene Bobo?

Bobo dan ajin su Aliya ne a makaranta, shine wanda yayi mata kyauta a ranar masoya wato (Valentine’s Day), ya taba zuwa bakin ruwa tare da wata Budurwa mai suna Morayo.

Waye Akin?

Akin dan Ajin su Aliya ne a makaranta, dalibine mai kokari/kwazo sosai da sosai, sannan yana da yawan abin dariya da nishadi.

Wacece Miss Salako?

Miss Salako itace Malamar Lissafi (Mathematics), wadda ta hukunta Akin saboda yazo da wasa alokacin da take darasi a aji.

Waye Bunmi?

Shi kuma dan makarantar su Aliya ne, amman ya wucesu a aji, kuma shine mai tsokana/kyarar Aliya a makaranta.

Wacece Malamar Biology?

Malamar Biology tana yabon Aliya, sunan malamar shina Fatima

Waye Zak?

Zak dalibine mai kokari wanda ana alfahari dashi a makarantar, shine ya baiwa Aliya rubutaccen sakon soyayya.

Wace Grace?

Grace dakinsu daya da Aliya bata da yawan magana, mutane na mata kallon girmankai da wulakanta mutane.

Wacece Bisi?

Itace yarinyar da ta dage wajen ganin ta hana Aliya zuwa ofishin Principals.

Waye Sogo?

Sogo ‘yar ajin su Aliya ce mahaifinta yace sai tazama Lawyer tunda shima Lawyer ne.

Rubutuka Masu Alaka:

Abinda yasa dalibi zaici Jamb da Post UTME sannan ya rasa samun Admission

Menene Banbancin Jamb, UTME, da Post UTME?

Matsalolin da ake fuskanta wajen yin register Jamb

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!