Katin Zabe Da Yadda Ake Yinsa

Home Government Issues Katin Zabe Da Yadda Ake Yinsa
Katin Zabe Da Yadda Ake Yinsa

Katin Zabe Da Yadda Ake Yinsa

Menene Katin Zabe?
Katin Zabe (Voters Card) shine katin da zai baiwa duk wani dan Nigeria mai shekaru Sha Takwas (18) zuwa sama damar kada kuri’ar sa a matakan zaben Shugaban kasa, Gwamna, ‘Yan Majalisun jiha, tarayya da Dattijai, shugaban karamar hukuma da Kansiloli.

Abubuwan Da Ake Yi Da Katin Zabe
Baya ga yin zabe kuma ana amfani da katin zabe wajen register wani abu na hukumomi, ko bankuna da sauran duk wani abu da ake yi da Valid ID Card.

Su Waye Ke Yin Katin Zabe?
Hukumar zabe ta kasa itace ke da alhakin yiwa ‘yan kasa katin zabe.

Ana Biyan Kudi Domin Yin Katin Zabe?
A’a katin zabe kyauta ne ba’a bada ko sisi duk wanda ya karbi kudinka da sunan katin zabe to ka wurgashi ga mahukunta.

Su Waye Ya Halatta Suyi Katin Zabe?
Duk wani dan Nigeria da ya kai shekara 18 zuwa sama to shine ke da ‘Yancin yin katin zabe.

Yaushe Ake Yin Katin Zabe?
Yanzu ba kamar shekarun baya ba da ba’a yin katin zabe sai lokacin da zabe ya karato a’a yanzu kowane lokaci mutum yake so zaije yayi, sai dai kawai yanzu an dakatar har sai bayan zaben 2019 za’a cigaba da yi.

Yaya Ake Yin Katin Zabe?
1. Zakaje ofishin hukumar zabe na karamar hukumar ka.
2. Zasu duba suga shekarunka sun kai? Idan basu gamsu ba musamman irina masu karamin jiki to za’a ce ka kawo Takardar Shaidar Haihuwa.
3. Za’a baka foam ko lamba.
4. Ana bin layi saboda yawan mutane (a baya).
5. Za’a shigar da bayanan ka.
6. Za’a yi maka hoto.
7. Zakayi thumb print.
8. Sai a cire maka katin zabe na wucin gadi (temporary voters card).

Yadda Zaka Karbi Katin Zabenka
Bayan ka karbi katin zabe na wucin gadi to zaka dan jira kadan, sai dai shi ba kamar katin dan kasa ba, baya jimawa sosai.
Zaka iya dubawa ta website din INEC domin ganin ko katin ka ya fito? Wani lokacin kuma suna bada sanarwa cewa daga wata kaza zuwa wata kaza wadanda sukayi katin zabe to katinsu ya fito sai kaje ka karba.

A watannin baya kadan na samu tattaunawa da Jami’in hurda da jama’a na hukumar Zabe ta Jihar Kano Malam Garba Lawal Muhammad kuma ya tabbatarmin cewa yanzu haka suna da dubunnan katinan zabe a ajiye masu shi basu zo sun karba ba.

Allah Ya Taimaka.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
December, 2018.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!