[Karanta Yanzu] Matsalolin Da Ake Fuskanta Wajen Yin Register Jamb

Home JAMB [Karanta Yanzu] Matsalolin Da Ake Fuskanta Wajen Yin Register Jamb
[Karanta Yanzu] Matsalolin Da Ake Fuskanta Wajen Yin Register Jamb

Jamb 2019/2020

Kashi Na 03

(23-12-2018)

Marubuci: Ismail Saleesu Ali (Arewa Students Orientation Forum)

Rajistar Jamb da Matsalolin da ake Fuskanta

JAMB dai Dayace daga cikin hanyoyin Shiga Jami’a, da makarantun Gaba da Sakandare a Nigeria, (Tertiary Institutions) Kuma Bugu da Kari JAMB
itace babbar Hanyar da ake bi ashiga Jami’a.

Matsalolin da ake fuskanta a lokacin rajistar Jamb

Tabbas dalibai suna Fuskantar matsaloli masu tarin yawa a lokacin rajistar jamb, wanda matsalolin sun hada da:-

1-Date Of Birth

2-Home Town

3-Gender

4-UTME Combination

5-Name/Typing Error

6 – E-MAIL Address

da sauran su.
Wadannan Matsalolin a Dunkule, Suna Faruwa ne a Lokacin da mutum yake yin Rajistar JAMB dinsa, Sakamakon sauri wurin ganin anyi an gama mashi, ko kuma Rajistar JAMB din a wajen wanda basu kware ba. Faruwar Daya daga cikin Matsalolin zai iya kawo maka matsala ko kuma ya tilasta maka biyan Kudin Data Correction. Misali:
A Lokacin Rajistar JAMB dinka kai namiji ne amma sai aka sa maka Female, ko a sanya maka Email mara kyau, ko kuma a Chanja maka jihar da kake, ko Ranar Haihuwa. Kamar an haifeka a 1st January, 1998 misali, sai a saka maka 1st January, 1989.
Wadannan Matsalolin dole sai dalibi Ya Lura sosai a Lokacin Rajistar JAMB dinsa dan Kauce musu.
Abu na farko da zakayi shine Lokacin da zakayi Rajistar ta jamb kanutsu sosai, kuma abaka Form kacika, Sannan duk abunda ka manta yadda yake to kar ka cika da ka, kabari sai ka tabbatar. Kamar Misali: Kana Shakkar Shin a watan May ne aka haifeni ko March, to kar ka cika kabari saika tabbatar da watan ta hanyar duba Birth Certificate dinka. Bayan ka gama cika Form din kuma sai kasa ido sosai akan monitor (Allon kwamfiyutar) Domin Kaucewa Matsalolin. Sannan duk abunda ka gani an rubuta maka ba dai-dai ba to kar kayi shiru kayi magana a gyara maka. Wannan kenan.
Sai kuma Matsalolin da dalibai ke Fuskanta bayan kammala Rajistar JAMB dinsu. Matsalolin sun hada da:-

1-Manta E-Mail password

2-Manta Profile code

3-Faduwar Slip

4-Rashin Sanin Gurin Jarrabawar

5-An turani Wani Gari bansan inda zan kwana daya ba

da sauran wasu matsalolin. Tabbas Wadannan Matsalolin Suna Tada Hankalin Dalibai ainun.

Dan haka da yardar Allah Zamu Dauki Kowacce Matsala Daya Bayan Daya Muyi cikakken bayani akai, ta yadda za’a kaucewa matsalar, da kuma yadda za’a magance ta idan ta faru, Insha Allah.

Kukasan Ce Tare Da Kungiyar ASOF a Koda Yaushe, dan Sanin Halin da Ilimi yake a Kasar

Mungode

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!