[Karanta Yanzu] Abubuwan Da Yakamata Ka Sani Kafin Kayi Register Jamb

[Karanta Yanzu] Abubuwan Da Yakamata Ka Sani Kafin Kayi Register Jamb

Jamb 2019/2020

Kashi Na 02

Marubuci: Ismail Saleesu Ali (Arewa Students Orientation Forum)

– Ranar 10th January, 2019 za’a fara Siyarda Form Na Jamb

– Sati Shida Kacal za’ayi ana Siyar wa

– JAMB Ba Za Ta Amince Da Ci Gaba da yin rajistar UTME (Jamb) a Kafe ba

Hukumar shirya jarabawar Share fagen shiga Jami’a, wato (Jamb) ta ce za ta fara siyar da fom din na Jamb ne daga ranar 10 ga watan January, 2019. Hukumar ta Jamb ta bayyana hakan ne a lokacin wani taro da ya gudana tsakanin ta da cibiyoyin ilimin komputa da ke Jami’ar Legas, ranar Alhamis dinda ta gabata. Hukumar ta Jamb ta bayyana cewa bazata lamunci yin rajistar jamb din ba a kowanne Kafe/Cafe. Shugaban hukumar ta JAMB, Prof. Ishaq Oloyede ya ce daga yanzun ba za’a ci gaba da yin rajistan na UTME (jamb) ba a kowane cibiyoyin Cafe, sai dai a wurare na musamman da muka kebe. Prof. Oloyede, ya bayyana cewa, kayyade wuraren yin rajistan an yi shi ne ba dan komai ba sai dan a magance yanda ake chajin dalibai masu yin rajistan kudaden da ba su kamata ba, da kuma yadda ake hargitsa sunayen daliban dama sauran wasu cuwa-cuwa na daban wanda hakan yake kawowa dalibai cikas. “Daga Yanzu, duk wasu ayyuka makamantan hakan, kamar na yin rajistar Jamb din, daura sakamakon jarabawar WAEC da ta NECO, (Uploading Results) daukan bayanan dalibai duk a wuraren da muka kebe ne na musamman za a rika yin su domin rage yanda ake hargitsa abun, haka kuma wadanda sukayi jarabawar za’a iya tantance bayanan su ta hanyar dangwala yatsun su kafin a fitar da su” (thumbprint) inji Prof. Oloyede. Hakanan Prof. din ya shawarci wuraren da aka keben da su inganta ayyukan na su da kyau, domin su gujewa amshe lasisin da Hukumar ta Jamb din ta basu. “Duk da cewa kashi 80 na wadannan cibiyoyin da muka kebe sun taka rawar gani matuka a shekarar 2018. Amma mun dakatar da wasu wadanda aikin nasu bai yi kyau ba. Mun dakatar da cibiyoyi 50 daga yin rajistar a wannan shekarar ta 2019, kuma Yanzu muna da cibiyoyi 718 da zamuyi aiki dasu. Danganeda lokacin da za’a dauka ana siyar da form din Prof. Oloyede yace, za’a siyar da Fom din ne har tsawon sati shida. Akan batun Babban zabe na kasar Chairman na Hukumar ta Jamb ya bayar da tabbacin cewa zaben na 2019 ba zai shafi tsarin jarabawar ba.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!