[Ka Ranta Yanzu] Abinda Yakamata Ka Sani Game Da Hukumar Jamb

Home JAMB [Ka Ranta Yanzu] Abinda Yakamata Ka Sani Game Da Hukumar Jamb
[Ka Ranta Yanzu] Abinda Yakamata Ka Sani Game Da Hukumar Jamb

Jamb 2019/2020

Marubuci: Ismail Saleesu Ali (Arewa Students Orientation Forum)

Kashi Na 01
Tarihin Hukumar Jamb:-
Joint admission and matriculation Board (JAMB)
Wannan hukuma cibiyace ta shirya jarabawar Share fagen shiga Jami,a tare da sauran cibiyoyin ilimi aduk fadin Nigeria kamar irinsu Polytechnics da Colleges, kuma mutum zaisamu damar yin jarabawar ne matukar dai ya kammala karatunsa na sakandare.
Shiga Jami,a kafin akirkiri hukumar jamb:-
Kafin akirkiri Hukumar jamb Nigeria tanada jami,O,I ne guda shida zuwa bakwai a shekarar 1974 kenan. Kowace jami,a daga cikinsu tana shirya jarabawarta ne kuma tadauki adadin daliban da sukayi Nasarar cin jarabawar. Ana cikin hakan karkashin jagorancin mulkin Chief Olusegun Obasanjo a shekarar ya kara kirkirar wasu jami,o,I guda shida (6), bayan haka kuma sai gwamnatin ta kafa wani kwamiti dazai rika kula da jarabawar ta shiga jami,a karkashin shugabancin Mr. M. S Angulu.
Bayan haka sai wannan kwamitin ya bada shawarar akafa wasu hukumomi guda biyu, wato; CENTRAL ADMISSION BOARD da kuma JOINT MATRICULATION BOARD. Gwamnatin mulkin soja na wannan lokacin ta amshi shawarorinda kwamitin ya bata inda ta kirkiri JOINT ADMISSIONS AND MATRICULATION BOARD, daga nan sai aka kafa hukumar a shekarar 1978, 13th February, A karkashin dokar kundin tsarin mulkin soja ta Nigeria shekarar 1978. (Decree No. 2 of the federal military government of Nigeria)
Hakanan a shekarar 1988 watan August akayi gyara a kundin tsarin mulkin sojan No. 2 decree, Inda aka basu iko da damar shirya jarabawar domin shiga makarantun Polytechnics da Colleges of Education a duk fadin Nigeria.
Sannan wannan gyaran (Amendments) tun lokacin aka tsarashi aka rubutashi cikin kundin tsarin mulki na soja (Decree No. 33 of 1989, Of the federal military government).
To ko yaya akeyin Jarabawar ta Jamb ?
Ada anayin jarabawar ta jamb ne da takarda da pencil inda ashekarar 2012 Registrar na jamb awannan lokacin ya bada sanarwar cewa yanzu jarabawar zata kasance ne ta dayan hanyoyi uku;
1• Pepar and Pencil Testing (PPT)
Inda za,ayi jarabawar da takarda da pencil
2• Dibu Based Test (DBT)
Inda za,a kawo tambayoyin a kwamputa amma sai a amsa su a takarda
3• Computer Based Test (CBT)
Shikuma anan da tambayoyin da kuma amsasu duka zai zamane a cikin komputa din.
Hakan ya farune sakamakon wasu da dama daga cikin dalibai suna rasa sakamakon jarabawar tasu saboda bacewar takaradar da suka amsa jarabawar.
Hakanan wannan jarabawa anayinta ne sau daya ashekara inda akowace shekara ake samun kimanin dalibai miliyan daya da suke zaunawa jarabawar. Kuma jarabawar tanada darasi hudu ne; (1) English Language Wanda dolene sai kowanne dalibi yayishi, saikuma sauran darasi uku dasukeda alaka da kwas (Course) dinda kakeso kakaranta a jami,ar, sannan jarabawar tana dauke da tambayoyi guda dari biyu da hamsin (250) inda English yakeda tambaya 100, sauran darusa ukun kuma sunada hamsin hamsin (50) amma a shekarar 2017 anrage yawan tambayoyin inda aka dawo dasu 180 English 60, sauran darusan kuma 40 sannan kuma jarabawar a shekarun baya tanada lokacine dayakai tsawon awa uku da minti goma, (3 hours, 10 minutes) amma shima anrage inda aka mayardashi awa biyu kacal, (2 hours) amma adadin maki din jarabawar yananan yadda yake bai canja ba wato (400 Marks).
To maki nawa akeso mutum yaci a Jamb din ?
Maki mafi karanci da akeso dalibi ya samu shine 180, inda a Shekarar 2007 maki din yake 160, a shekarar 2008 kuma aka karashi yazama 170, kana kuma a shekarar 2009 aka mayardashi 180, a 2017 aka dawo dashi 120 a 2018 Kuma aka mayar dashi 140, amma a wannan Shekarar ta 2019 bamusan nawa ne zasu ce ba, Sakamakon sai Hukumar ya jamb ta zauna da duka wakilan Jami’o’i da kwalejoji da sauran su dan tattauna nawa ya kamata a saka, hakan kuma yana zuwa ne bayan an gama jarrabawar ta Jamb.
(Amma kusani kowace university tanada adadin maki dinda takeso, ya danganta ne da irin kwas dinda kakeso kakaranta. Ba lallai ne Dan kaci 180, ko140 ba kasamu admission)
Yaya zanyi in shiga jami,a ta hanyar jamb ?
Wannan abune mai sauki, kawai abinda zakayi shine kaje ka bude profile a shafin yanar gizo na jamb din daganan saikaje banki kabiya kudi, su kuma bankin zasu baka wata lamba da akecema e-pin, to idan suka baka saikaje daya daga cikin ofishin hukumar ta jamb dan yimaka rajista kokuma kaje daya daga cikin centers din da hukumar ta basu lasisin yin jarabawar. Idan zakatafi saikaje da O’ level dinka (Waec/Neco/
Nbais/Nabteb) sannan katabbata kaci darasin English da ilimin lissafi (Mathematics) kuma katabbata kaci darasin da yakeda alaka da kwas dinda kakeso kakaranta a jami,ar.
To daganan idan lokacin jarabawar yayi zasu sanar daku, kuma katabbata kaci maki dinda baigaza Wanda ake Bukata Ba, To idan Kayi nasarar cin jarabawar jami,ar da kanema zata baka admission inda zaka fara daga aji daya, (Level 100/Level 1/ UG 1) to shikenan ka shiga jami,a.
Sannan zaka shekara hudu idan kwas din mai shekara hudu ne, kokuma biyar idan mai shekara biyar ne.
References:-
1• USING ASSESSMENT FOR THE IMPROVEMENT OF TERTIARY EDUCATION IN NIGERIA: THE JOINT ADMISSIONS AND MATRICULATION BOARD (JAMB)
ROLE. BY:
PROF. ‘DIBU OJERINDE (REGISTRAR/CE) JOINT ADMISSIONS AND MATRICULATION BOARD (JAMB), ABUJA, NIGERIA.
2• JOINT ADMISSIONS AND MATRICULATION
BOARD ACT
3• Www.jamb.gov.ng
4• Sahara Reporters (Sep. 25, 2008)

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!