Yadda Zaka Kayi Rubutu Da Hausa A Baka N30,000

Home Government Issues Yadda Zaka Kayi Rubutu Da Hausa A Baka N30,000
Yadda Zaka Kayi Rubutu Da Hausa A Baka N30,000

Author : Al’amin Jamil Musa

Shin Kana da Damuwa Da Yadda Ake Gudanar Da Ayyukan Gwamnati A Inda Kake, Kuma Ba Ka da Damar Daukan Mataki Akai?

Ko Kuma Aikin Rashawa Ka Gano Ka Ke Son A Magance Shi A Matsayin Ka Na Me Kishin Kasa .

In kuwa haka ne toh, kwantar da hankalin ka don kuwa cibiyar nan ta bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato( CITAD) da taimakon gidauniyar MacArthur sun shirya tsaf don kawo karshen wannan damuwar taka ta hanyar isar da damuwar ka ga mahukunta.

Sun samar da wani sabon tsari mai suna “Report a Project” shi ne sabon tsarin da wadannan cibiyoyi suka bullo da shi don kawo karshen wulakantar da ayyuka da gwamnatoti ce kiyi , ko kuma yin su bada inganci ba dama uwa uba batun bankado badakalar cin hanci da rashawa ta hanyar baiwa matasa dalibi damar shigar da rahoton duk wani batun dake da alaka da abin da muka ambata a baya.

Abin sha’awa kuma shine zaka iya rubutawa da tura rahotanka cikin harshen Hausa ko Turanci English.

TAGOMASHIN DA ZAKA IYA SAMU SAKAMAKON YIN WANNAN AIKIN:
In rahotan ka yai nasarar zamo wa mafi kyau akwai kyauta gwaggwaba. N30,000 wani kuma zai samu N20,000
Bugu da kari za’a sanya rahotan naka a cikin shirin da za’a gabatar a gidan rediyo.

Domin tura naka rahoton zaka sai ka danna kasa 👇
http://www.reportaproject.ng

Allah ya bada sa’a ya taimaki kasar mu Najeriaya

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!