[Sabon Labari] Kungiyar Dalibai Ta Kasa Ta Baiwa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Zuwa 31, December 2018 Kan Su Sulhunta Kansu.

Home News [Sabon Labari] Kungiyar Dalibai Ta Kasa Ta Baiwa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Zuwa 31, December 2018 Kan Su Sulhunta Kansu.
[Sabon Labari] Kungiyar Dalibai Ta Kasa Ta Baiwa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Zuwa 31, December 2018 Kan Su Sulhunta Kansu.

[Sabon Labari] Kungiyar Dalibai Ta Kasa Ta Baiwa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Zuwa 31, December 2018 Kan Su Sulhunta Kansu.

Shugaban kungiyar dalibai ta kasa NANS Umar Farouq Lawal shine ya bayyana haka a yayin ganawarsa da manema Labarai yau a Abuja.

Jaridar Vanguard ta rawaito Umar Farouq ya zargin bangarorin biyu da yunkurin kawo tasgaro ga babban zaben shekara ta 2019 dake karatowa.

“A yau muna so mu sanarwa da gwamantin tarayya da kungiyar ASUU cewa bama tsoron kowa, kuma mun shirya daukar matakin zanga-zangar lumana da zamu rufe filayen jiragen sama da kuma manyan hanyoyin kasar nan”

“Muna jan hankalin gwamnatin tarayya ta sani cewa da yawa daga shuwagabannin kasarmu sunyi karatu a kyauta, a dai-dai lokacin damu muke biyan kudin makaranta kudin takarda da kudin wurin zama”

Shugaban NANS ya kara da cewa “abun mamaki ne wasu mutane su dinga Ikrarin gwamnatin tarayya tayi wani abin azo a gani a bangaren ilimi, dai-dai lokacin da wannan abun ban takaicin ke faruwa”

“Ina son wannan sakon yaje har teburin shugaban kasa, kuma ya sani zaben 2019 yana dab da karatowa kuma dukkan kuri’ar daliban Nigeria ba zamu zabi gwamnatin da bata kula da harkar karatunmu ba”

“Idan basu sasanta kansu zuwa 31, December 2018 to mu zamu dai-dai ta su”

Allah ya kyauta.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
December, 2018.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!