[Karanta Yanzu] Ka San Abinda Ake Nufi Da Valid ID Card?

Home Awareness [Karanta Yanzu] Ka San Abinda Ake Nufi Da Valid ID Card?
[Karanta Yanzu] Ka San Abinda Ake Nufi Da Valid ID Card?

Ilimantarwa: Shin ko kasan me ake nufi da valid ID Card?

Author: Al’amin Jamil Musa

Mai karatu barka da warhaka da fatan kana jin dadin kasancewa da mu.
Nasasn sau da dama me karatu kan tsinci kanshi a wani yanayi ko halin da za’a bukaci ya gabatar da shaidar da zata nuna ko shi wanene, wato dai ma’ana ID card. Musamman a duk lamarin da ya shafi kasa baki daya, kamar guraren daukan aiki, bada tallafi, bude asusun ajiya na banki, da dai duk wani abu me muhimmanci. Kuma kurum sai ka ji an ce Valid ID card ake da bukata, nan take sai kaga mutum na kokarin gabatar da ID Card din san na makaranta, kasuwa, gurin aiki da dai sauransu a matsayin valid ID Card tun da shi a tunaninsa ai ID Card din da lokacin aikin sa me kare ba wato (Expire ) shi ne valid, wanda kuwa lamarin ba haka yake ba.

IN KUWA BA HAKA BANE WANNE NE?
Yauwa! Yanzu zaka ji batu.

VALID ID CARD:
Shi ne dukkan wani kati da gwamnatin tarraya ta samar a matsayin shaidar ka na gudanar da wani la’amari.
KO WANNE A CIKIN WADANNAN SHI NE VALID ID CARD:
1) PVC( katin zabe na din-din-din)
2) NIN ( katin dan kasa)
3) DRIVER’S LICENSE( shaidar bada izinin tuki)
4)INT.Passort (shaidar bada izinin fita daga kasa)

Wannan shine karshen bayani kan abin da ake nufi da Valid ID CARD muna fatan an ilimantu da abin da aka ji.
Mun gode!!!

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!