[Karanta Yanzu] Yadda Zakayi Idan WAEC Original Result Dinka Ya Bata

Home Exam's [Karanta Yanzu] Yadda Zakayi Idan WAEC Original Result Dinka Ya Bata
[Karanta Yanzu] Yadda Zakayi Idan WAEC Original Result Dinka Ya Bata

[Karanta Yanzu] Yadda Zakayi Idan WAEC Original Result Dinka Ya Bata

Jama’a Assalamu alaikum a yau zamuyi magana akan yadda mutum zaiyi idan WAEC Original Result dinsa ya bata, sai a biyomu.

Idan ka duba jikin WAEC Original result zaka ga an rubuta cewa idan har ya bata to WAEC ba zata kara baka wani irin wannan result dinba.

Haka kuwa abin yake indai ka batar dashi to WAEC din zata shafawa idonta toka tayi halin ba sani ba sabo domin kuwa ba zata baka wani irin wannan sakamakon ba.

Duk sanda wani abu ya taso maka da wani organisations ko hukumomi ke bukatar wannan result din to sai dai su rubuta takardar nema ga Hukumar WAEC, bayan wani lokaci hukumar WAEC zata aikawa da wannan organisation ko hukuma cewa Wane-wane tabbas yayi wannan jarrabawar da kuma karin bayani a rubuce, duk sanda mutum yake bukata sai yayi wannan tsarin.

A shekarar 2015 Hukumar WAEC ta canja sabon tsari cewa idan takardar ka ta bata.
Sabon tsarin 2015 shine mutum zai tafi hukumar WAEC ka sana musu cewa WAEC dinka fa ta bata.
Zaka tafi da hoton passport guda biyu.
Zaka cike form sannan ka biya N20, 000, WAEC zata buga maka sabon result irin wanda ya bata, ana kiran wannan result din da “Attestation” zaka ga an rubuta a jikinsa da jan biro, banbancin su kenan da na asalin.

Wannan itace hanyar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yabi aka dawo masa da sakamakon jarabarwar sa da ya bata, sai dai shi Baba Buhari har Office aka kai masa, kai kuma babu wanda zai kawo maka har gida.
Zaka jira har WAEC ta gama sannan ta aiko da ita jiharka sai kaje ka karba shikenan.

Shawarata ga wanda jarrabawarsa ta bata:
1. Mutum yaje yayi police report.
2. Sannan yayi court affidavit.

Allah ya kiyaye batan jarabarwarmu Amin.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist
12-12-2018.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!