[Karanta Yanzu] Dalilin Da Yasa Dalibi Zaici Jamb Amman Ya Rasa Samun Admission

Home Admission [Karanta Yanzu] Dalilin Da Yasa Dalibi Zaici Jamb Amman Ya Rasa Samun Admission
[Karanta Yanzu] Dalilin Da Yasa Dalibi Zaici Jamb Amman Ya Rasa Samun Admission

[Karanta Yanzu] Dalilin Da Yasa Dalibi Zaici Jamb Amman Ya Rasa Samun Admission.

Da yawa dalibai suna yin kuka da wannan matsalar cewa sunci jarrabawar Jamb amman kuma gashi basu samu admission ba, to ‘yan uwa ko kun san me yake jawo wannan matsalar?

Dalilin shine:- a shekarun baya zata iya kasancewa Jamb bata baka admission ba amman makaranta sai ta baka, amman yanzu al’amarin ba haka yake ba, indai ka ga Jamb ta baka admission to tabbas makaranta ta baka haka idan jamb bata baka ba to makaranta bata baka ba.

A yanzu babu yadda za’ayi Jamb ta baka admission har sai makaranta ta baka, dama can rashin tsarina ya sanya Jamb ke bada admission ba tare da sahalewar makaranta ba.

YADDA TSARIN YAKE A YANZU SHINE:

Idan makaranta ta gama tattara Admission list dinta sai ta aikawa da Jamb, to daga nan ana sa ran Jamb zata dora sunayen daliban duka akan portal dinta, idan ta gama dorawa sai makaranta ta duba domin tabbatar da abinda ta bayar shine aka saka.

Shine sai makaranta ta fitar da nata sunayen idan kaje karbar admission letter na makaranta to ba za’a baka ba har sai ka nuna Jamb Admission Letter.

Rubutuka Masu Alaka:

JAMB: {YADDA ZAKA BUDE JAMB PROFILE 2019/2020}

Yaushe Za’a Fara Register Jamb 2019?

Yadda Zaka Samu Maki 270+ A Jamb

KA SAN ME YASA WASU KO AN TURAWA JAMB BATA SAKA SUNANSU A PORTAK DINTA?

A lokacin da ake register Jamb akwai wurin da ake saka WAEC/NECO to kuma sai an fara yin Jamb sannan ake yi su NECO/WAEC don haka mutum baya sakawa sai dai in wanda daman ya riga yayi NECO/WAEC dinsa.

To Jamb tana jiran idan sakamako ya fito dalibi yaje ya saka mata wadannan result din nasa na NECO/WAEC a portal dinta, to idan bai saka ba ita kuma ba zata taba bashi Admission ba koda yaci jarabawar Jamb.

A shawarce dalibi ya dinga duba portal dinsa na jamb musamman a lokacin da yaji makarantar da ya nema sun fara admission.

A wannan shekarar ma an samu wani matsalar daga wasu dalibai amman bayan mun fada musu su hau su saka NECO/WAEC kuma suna sakawa suka samu admission dinsu, suka cire kuma sukaje makaranta suka nuna aka basu na makaranta.

Allah ya bada sa’a.

Basheer Sharfadi

Social Media Startegist.

10-12-2018.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!