Yadda Zaka Karbi Kudin Trader Moni {10,000} Dinka Na Farko Ta Wayarka

Home News Yadda Zaka Karbi Kudin Trader Moni {10,000} Dinka Na Farko Ta Wayarka
Yadda Zaka Karbi Kudin Trader Moni {10,000} Dinka Na Farko Ta Wayarka

Da yawa mutane suna tambayar shin yaya zasu fitar da kudinsu daga kan layukan wayansu, da kuma yadda zasu mayar da kudin trader moni.

Acikin wannan bayanin zanyi bayanin yadda wannan tsarin yake.

KA KARANTA WANNAN?: YADDA ZAKA NEMI RANCEN KUDI N300,000 ZUWA SAMA DAGA GWAMNATIN TARAYYA –FARMER MONEY

  1. Menene Mobile Wallet kuma yaya ake amfani dashi?

Mobile Wallet shine tsarin da zai baka damar sarrafa kudi ta hanyar karba da kuma aikawa da kudi, ko siyan katin waya siyayyar kaya a internet da makamantansu ta wayarka ta salula, ba tare da wani katin ATM ko makamancinsa ba.

Wato dai Mobile Wallet tamkar wani account ne na banki amman wanda zaka budewa wayarka ta salula lambarka a matsayin Account Number.

KA KARANTA WANNAN?: YADDA ZAKA TUNTUBI JAMI’AN TRADER MONI NA YANKINKA

N10,000 da ake biya na Trade Moni ana biyansa ne a tsari na Mobile Walled, daga nan kuma sai mutum yayi transfer don cire kudinsa ta hanyar bankin da yake son cira.

Domin karin bayani sai ka ziyarci www.tradermoni.ng

KA KARANTA WANNAN?: YADDA ZAKA ZAMA JAMI’IN TRADER MONI

Zuwa karshen watan December ana sa ran tsarin trader moni zai amfani masu kananan sana’o’i kimanin Miliyan Biyu a jiho 36 da birnin tarayya Abuja, kowace jiha ana sa ran mutane 30,000 zasu amfana da tsarin.

Tun bayan kaddamar da Tsarin Trader Moni al’umma da dama ke amfanuwa da tsarin a sassa daban-daban na kasar nan.

 

KA KARANTA WANNAN: YADDA ZAKA MAYAR DA RANCEN TRADER MONI DA KA KARBA

 

Allah ya bada sa’a.

 

 

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!