Nigerian Defence Academy (NDA) Ta Fara Dibar Sabbin Dalibai

Home Admission Nigerian Defence Academy (NDA) Ta Fara Dibar Sabbin Dalibai
Nigerian Defence Academy (NDA) Ta Fara Dibar Sabbin Dalibai

MAKARANTAR HORAR DA AIKIN SOJI WATO ‘’NIGERIAN DEFENCE ACADEMY’’ TA BUDE SHAFINTA NA YANAR GIZO DOMIN DAUKAN SABABBIN DALIBAI MASU KARATU A CIKAKKEN LOKACI A KARO NA SABA’IN DA DAYA

TAKARDAR NEMAN SHIGA :
1. Hukumar makarantar horar da sojoji ta Nigeria wacce akafi sani da NDA tana sanar da Al umma cewa ta bude shafinta na yanar gizo domin daukan sababbin dalibai masu san karanta darasi na musamman a cikakken lokaci a karo na sabain da daya, inda za’a fara neman gurbin shiga daga ranar litinin 22 ga watan octoba 2018 zuwa ranar Alhamis 14 ga watan Mayu 2018.

Damar shiga makarantar ta hada da maza da mata,ga masu sha’awar shiga sai su ziyarci shafin makarantar ta www.nda.edu.ng ko kuma ta RCapplications.edu.ng
Kudin neman izinin shiga naira Dubu uku da dari biyar ne kacal (#3500.00)
2. NOTE: Hanyar biyan kudi ta RRR Codes ta hanyar shafin neman shiga makarantar kadai aka yarda dashi .

YADDA ZAKA NEMI GURBIN SHIGA MAKARANTAR SHINE:
3. Ga dalibai masu sha’awar shiga makarantar sai su ziyarci shafin makarantar wanda akai bayani a sama domin su cike bayanansu da ake bukata,sannan su sauke (Downloading) Dokoki da kaidojin makarantar su kuma karanta shi a tsanake cikin nutsuwa.
Duk dalibin da zai nema ya tabbata ya nemi makarantar ta hanyar hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami’oi wato JAMB sannan ya nemi makarantar a matsayin zabinsa na farko wato (First choice), bayan haka kuma wajibi ne ya zama darasin da ya zaba a shafin makarantar dana JAMB ya zama iri daya.Bayan haka kuma akwai bukatar ya zauna rubuta jarrabawar UTME da hukumar JAMB ke shiryawa.

TURA BAYANAN TAKADDUN DA AKA NEMA:
4.Takaddun da aka cike zaa tura su ne tare da hoton sakamakon jarrabawar gama sakandire wato SSCE zuwa shafin makarantar na yanar gizo.Sannan bayan tura takaddun dalibi ya tabbata ya mallaki kwafin bayanan da ya cike yayin nema wato (Acknowledgement Form).

ABUBUWAN AKE BUKATA KAFIN SAMUN GURBIN SHIGA :
5. Abubuwan da ake bukata ga masu son karantar matakin karatu na ‘’Degree’’ anyi bayaninsu a shafin makarantar na yanar gizo,haka sauran bayanai da suka hada da darussan da za’a iya karantawa na ‘’Degree can-cantar samin gurbin karatu da kuma jarrabawar tantancewa duk anyi bayanin su a shafin makarantar na yanar gizo.

6. NOTE:Ga masu takardun karatu na yarukan faransanci,larabci da madari zai zamar musu Karin samun damar shiga makarantar.

Baza’a karbi sakamakon jarrabawar WAEC/NECO ko NABTEB na shekarar 2019 sai na kasa da shekarar.

KA’IDOJIN JARRABAWAR TANTANCEWA:
7. Kadai za’a dauki dalibin daya cika kaidojin neman shiga ne kuma yake da sakamakon jarrabawar JAMB mai maki 180 ga masu neman bangaren Arts & Social Sciences da Sciences da kuma maki 210 ga masu neman darussan Engineering Sannan za’a basu damar fitar da takardar shaidar cancanta zuwa wajen tantancewa wato (Screening Test Admission Card) Kuma sune zasu halacci jarrabawar wato (NDA Screening Test) a cibiyoyin da suka zaba.

RANAR YIN JARRABAWAR TANTANCEWA DA KUMA ABUBUWAN DA AKE BUKATA:
8. Za’a gabatar da Jarrabawar tantancewar a matakai daban-daban,daya daga cikin jarrabawar wato ‘’Post-UTME’ itace wacce za’a gabatar a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu 2019.
Ana bukatar kowanne dalibi daya can-canta da yazo gurin jarrabawa da abubuwa kamar haka:
1. Takardar shaidar neman gurbin shiga wato (Acknowledgement Form )
2. Takardar shaidar cancantar zuwa wajen tantancewa wato (Screening Test Admission Card )
3. Takardar sakamakon makin jarrabawar JAMB wato (JAMB result slip )
4. Hotuna guda biyu masu girma wato fadi da tsayi kamar haka (3.5 by 5 inches )
NOTE: Hoto ya zama yana dauke da abubuwa kamar haka a bayansa:Ya zama daga kirji zuwa kai, sannan yana dauke da sunan dalibi,lambar jarrabawarsa,jihar sa,gurin yin jarrabawarsa,darasin da yake son karantawa,da kuma sa hannusa.
6. Kadai ga daliban da suka sami nasarar cin jarrabawar gwaji ne za’a gayyata zuwa mataki na biyu na tantancewa wato (Armed Forces Selection Board ) bayan haka kuma za’a saki sunayen daliban da suka sami nasarar shiga wannan makaranta.

YANAYI DA KUMA TSAHON LOKACIN BADA HORO:
10. Daliban da aka dauka zasu karbi horon sojoji da kuma na makaranta kamar haka;
Ga masu neman matakin zama ‘’Officer cadets’’ zasu karbi horaswa tsahon shekara biyar a matsayin ‘’Nigerian Army Cadets’’ shekara hudu kuma a matsayin ‘’Nigerian Navy’’ da ‘’Nigerian Air Force’’
Bayan kamala horaswa zaa yaye dalibai da shedar girmamawa ta ‘’Degree’’ a matakan karatu kamar haka BSc,BEng,BA .Za kuma su sami damar shiga hukumomin tsaro daman daban na Nigeria.

GUDANARWAR HUKUMOMIN MAKARANTA:
11. Ga daliban dake karantar darussa na mazaunin cikakken lokaci a makarantar za’a dauki nauyin kudin gudanarwar su na makaranta hade da abubuwan bukata na aiki daga gwamnatin tarayyar Nigeria.

DOMIN NEMAN KARIN BAYANI:
12. Ga dalibai masu neman Karin bayani dangane da kayayyakin aiki ko takardun jarrabobin da suka gabata,hukumar makarantar ta tattatara musu tambayoyin da suka gabata tare da amsoshin tambayoyin a hade akan farashi mai sauki wadanda zaa iya samun su ta hanyoyi kamar haka :
Shafin Yanar gizo: www.nda.edu.ng

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!