2018/2019 Yadda Zaka Nemi Aikin Dan Sanda

Home Government Issues 2018/2019 Yadda Zaka Nemi Aikin Dan Sanda
2018/2019 Yadda Zaka Nemi Aikin Dan Sanda

2018/2019 Yadda Zaka Nemi Aikin Dan Sanda

Hukumar ‘yan sanda ta kasa ta fara dibar sabbin jami’an ‘yan sanda na shekara ta 2018/2019 kwana kadan bayan da gwamnatin tarayya tayi karin albashi ga jami’an ‘yan sandan.

Abubuwan da ake bukata kafin daukar mutum sune:
1. Dole mutum ya zama dan Nigeria
2. Shekaru: Daga 18 zuwa 25.
3. Matakin Karatu: Daga matakin Sakandire Creadit 5 hade da Maths da English na WAEC, NECO ko NABTEB.
4. Ya zama ba’a taba samun mutum da aikata wani mummunan laifi ba.
5. Tsayi: Namiji kada ya zama kasa da Mata 1.67. Mace kuma kada yayi kasa da Mita 1.64.
6. Fadi: Kada yayi kasa da 86cm (34 inches).
7. Lafiya: ana bukatar mutum ya zama lafiyayye bashi da tarin tabo, ko zane, tattoos, matsalar gani ko mai ciki, da makamantansu.
8. Zaka sauke form da zaka cike bayanan Guarantors dinka guda biyu.
9. Sannan mutun zaiyi gwajin tabbatar da cikakkiyar lafiyarsa.

Yadda Zaka Yi Applying Shine:
1. Zaka nemi aikin ta yanar gizo (online)
2. Dole ya zama kana da Email da lambar waya mai aiki.
3. Sai ka ziyarci www.policerecruitment.ng
4. Zaka cike online form akai sannan kayi “submit” (ka kara dubawa da kyau kafin kayi submit)
5. Ka tabbatar kayi printing din sakon da zasu tura maka ta email bayan kayi submit din, sannan ka kwafi Registration Number dinka kayi saving dinta (Lambar tana da matukar muhimmanci a kula da ita sosai).
6. Zakayi printing Guarantors Form da ka cike kayi uploading ya zama kana da hard copy. Saboda idan kayi nasara dashi zaka je wurin screening.

Takardunnan da zaka yi scanning kafin fara cikewar sune:
1. SSCE: WAEC/NECO/NABTEB
2. Rigistar Haihuwa
3. Takardar Shaidar zama dan karamar hukuma.
4. Hotuna (passport).

Abubuwan Da Yakamata Ka Sani:
1. Babu email ko lambar da za’ayi amfani da ita sama da sau daya.
2. Duk wanda ya nema sama da sau daya za’a soke masa.
3. Za’a rufe neman ranar 15th January 2019.

Allah ya bada sa’a.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
01-12-2018.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!