Yadda Zaka Nemi Rancen Kudi N300,000 Zuwa Sama Daga Gwamnatin Tarayya

Home Government Issues Yadda Zaka Nemi Rancen Kudi N300,000 Zuwa Sama Daga Gwamnatin Tarayya
Yadda Zaka Nemi Rancen Kudi N300,000 Zuwa Sama Daga Gwamnatin Tarayya

*Yadda Zaka Nemi Rancen Kudi N300,000 Zuwa Sama Daga Gwamnatin Tarayya –Farmer Money*

 

*Menene Famer Money?*

Famer Money daya ne daga cikin tsarukan bada rance don bunkasa arzikin al’umma da gwamnatin tarayya ta kaddamar karkashin tsarin Government Enterprise and Empowerment Prpgramme (GEEP), ba tare da kudin ruwa ba sai dai 5% na tsarin gudanarwarsa.

 

*Ire-Iren tsarin GEEP:*

Tsarin bada rance na GEEP ya rabu gida uku (3) kamar haka:

 1. Famer Moni: Yana Farawa Daga N300,000
 2. Market Moni: Yana Farawa Daga N50,000
 3. Trader Moni: Yana Farawa Daga N10,000

*Abubuwan Da Kake Bukata Domin Samun Rancen GEEP:*

 1. Dole ka kasance dan Nigeria
 2. Dole ka kasance dan shekara 18 zuwa sama.
 3. Dole ya zama kana kasuwanci ko sana’a
 4. Ya zama kana da register da kungiyar sana’ar da kakeyi ko ta hukuma a yankinka.
 5. Ya zama kana da ID Card, katin Dan Kasa ko katin Zabe.
 6. Ya Zama kana da Bank Verification Number (BVN)
 7. Lambar waya wadda kayi register da layin da kanka.
 8. Email Address mai aiki.

 

Zaka iya yin register hadaka da tsarin Trader Moni ta hanyar shiga wannan link din: https://boi.ng/marketreg

 

Kungiyarku zata aika da bayananku ta wannan email din GEEP-States@boi.ng

 

KOWA YANA DA DAMAR YA NEMI RANCE DAGA GWAMNATIN TARAYYA

Bankin Masana’antu an samar dashi ne domin mu ‘yan kasa idan muna da bukatar rance muje domin mu bunkasa sana’armu.

 

Da yawa mutanenmu sukan gaza wajen cika sharadan da ake bukata, wanda abin ba haka yake ba a kudancin kasarnan.

 

Kowa yana da dama ya nema kaima kana da damar ka amfana da arzikin kasarka.

Idan kana bukatar rance daga gwamnati ka ziyarci https://www.boi.ng/ sai ka shiga APPLY FOR LOAN

*Kana Bukatar Register da Co-operate Affairs Commission (C.A.C):

Domin sanin yadda za kayi register da C.A.C kuma cikin saukin ragin kudin register da hukumar tayi Sai ka shiga wannan link din:

Yadda Zakayi Register Business Name Da C.A.C Akan N5,000 Kacal

 

*Yadda Zaka Nemi Rancen Famer Moni:*

 1. ka ziyarci boi.ng ko https://marketmoni.com.ng
 2. Sai ka shiga “Apply for loan now”
 3. Sai ka shiga “Register here to create account” zaka shigar da bayananka.
 4. A lokacin za’a tura maka da sakon link ta email dinka wanda zaka koma domin ka cigaba da yin register ta can
 5. Zaka koma email din ka shiga sannan ka karasa shigar da bayananka ka danna “Save” sannan “continue”
 6. Sai ka danna “submit”
 7. A sannan zasu aika maka da sabon sako ta email na cewa an karbi sakonka.

 

*Yadda Zaka Nemi Rancen Famer Moni Ta Hanyar Manhajar Eyowo:*

 1. Ka nemi jami’an Famer Moni a yankinka
 2. Ka karbi Form din Famer Moni ka cike bayananka
 3. Ka saka lambar wayarka
 4. Za’a tura maka da code wanda za kayi amfani dashi don tantance account dinka
 5. Daga nan zaka jira har kaji Alert a wayarka, sai ka nemi jami’an Eyowo don cirar kudinka.

 

*Jihohin da Aka Fara Bada Rancen Famer Moni Sune:*

Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nassarawa, Niger, Osun, Ondo, Ogun, Oyo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara, Abuja FCT.

 

Allah Ya Bada Sa’a.

 

Basheer Sharfadi

CEO research and awareness forum on internet Sharfadi.com

Email: info@sharfadi.com

WhatsApp: 09035830253

13-11-2018.

 

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!