Yadda Zaka Mayar Da Rancen Trader Moni Da Ka Karba

Home Government Issues Yadda Zaka Mayar Da Rancen Trader Moni Da Ka Karba
Yadda Zaka Mayar Da Rancen Trader Moni Da Ka Karba

*Yadda Zaka Mayar Da Rancen Trader Moni Da Ka Karba*

Jama’a da dama suna tambaya akan shin ta yaya zasu mayar da kudin da suka ranta karkashin tsarin Trader Moni.

*Yadda Rancen Trader Moni Yake*

Da farko za’a baka N10,000 kai kuma zaka mayar da N10,250 cikin ko kafin watanni shida (6) ita kuma Gwamnati zata sake baka N15,000.

Bayan ka karb N15,000 zaka mayar da N15,375 cikin ko kafin watanni shida (6) sai gwamnati ta sake baka N20,000.

Idan ka karbi N20,000 to zaka dawo da N21,000 cikin ko kafin watanni shida (6) gwamnati zata baka N50,000.

Idan ka karbi N50,000 zaka dawo da 52,500 cikin ko kafin watanni shida (6) gwamnati zata baka N100,000 ka mayar mata cikin watanni shida (6).

*Tsarin Mayar Da Kudin Shine:*

 1. Wanda ya karbi N10,000 zai dinga biyan N430 a duk sati har tsawon watanni shida.
 2. Wanda ya karbi N15,000 zai dinga biyan N640 a duk sati tsawon watanni shida,
 3. Wanda ya karbi N20,000 zai dinga biyan N875 a duk sati tsawon watanni shida.
 4. Wanda ya karbi N50,000 zai dinga biyan N2,187 a duk sati tsawon watanni shida.

*Note:* kana da damar mayar da kudin a yadda kake so ba sai a wannan tsarin ba, abinda ake bukata kawai ka mayar da kudin cikin lokaci.

*Yadda Zaka Mayar Da Kudin Shine:*

Zaka ziyarci daya daga cikin wadannan bankunan da zan jero a kasa sai kayi bayanin kazo biyan kudin Trade Moni, bankunan sune:

 1. Eco Bank
 2. Fidelity Bank
 3. GT Bank
 4. Heritage Bank
 5. Ja’iz Bank
 6. Stanbic Bank
 7. Starling Bank
 8. UBA Bank
 9. Union Bank
 10. Wema Bank

*Ta Yaya Zaka Sake Neman Trader Moni Din?*

Zaka sake nema kamar yadda ka nema a farko.

Allah Ya Bada Sa’a.

Basheer Sharfadi

CEO research and awareness forum on internet Sharfadi.com

Email: info@sharfadi.com

WhatsApp: 09035830253

13-11-2018.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!