Yadda Zakayi Register Business Name Da C.A.C Akan N5,000 Kacal

Home Government Issues Yadda Zakayi Register Business Name Da C.A.C Akan N5,000 Kacal
Yadda Zakayi Register Business Name Da C.A.C Akan N5,000 Kacal

A yanzu dai gwamnati tayi rangwame kan rijista da hukumar Corporate Affairs Commission wato (C.A.C) zuwa N5,000 sabanin tsuga-tsugan kudi da ake biya a baya, kuma wannan damar har zuwa karshen watan December na wannan shekara ta 2018.

 

YADDA AKE YIN REGISTER DA C.A.C SHINE:

Da farko zaka fara bude account a shafinsu, yadda zaka bude kuwa shine:

 1. Kaje https://services.cac.gov.ng
 2. Sai ka danna “Register”
 3. Zai bodo maka da form da zaka cike, babban abinda zaka lura anan shine, duk inda ka ga alamar “*” to dole ne sai ka cike wajen, sannan ka kula da duk abinda kake cikewa.
 4. Daga nan zasu tura maka da sakon tabbatarwa zuwa email dinka sai kaje kayi confirming shikenan ka bude account.

YADDA ZAKA YIWA KAMFANINKA REGISTER BUSINESS NAME:

 1. Zaka koma site din nasa
 2. Sai kayi Login
 3. Daga nan sai ka dan “Name Reservation”
 4. Sai ka shiga “Classification” sannan ka danna “Private Unlimited Company”
 5. Sai ka sanya sunan da kake son yin searching zasu baka dama ka sanya sunaye guda biyu 2 saboda idan baka samu daya ba sai ka samu daya.
 6. Sai ka danna “Save and Continue”
 7. Sai ka shiga “Reason for Availability Search” zaka zabi dalilin yin searching din sunan, akwai wurin kuma “Additional Information” idan kana da wani karin bayani zaka iya shigarwa a wajen, misali sauran batutuwan da kamfaninka ya kunsa.
 8. Sai ka danna “Save and Continue”
 9. Daga nan sai kuma biyan kudi sai ka danna alamar “Remita”
 10. Zai budo maka ka sanya bayanin katin ATM dinka.
 11. Daga nan sai “Send” da kuma “Cancel” sai ka danna “Send”
 12. Daga nan shikenan ka gama zaka jira, sannan ka dinga yin loading kana duba status na halin da ake ciki, idan an kammala zaka gani za kuma ka sauke receipt na Business Name dinka kaje kuma ka cigaba da Register kamfaninka.

Shikenan ka kammala.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!