Yadda Zaka Samu Maki 270+ A Jamb

Home Exam's Yadda Zaka Samu Maki 270+ A Jamb
Yadda Zaka Samu Maki 270+ A Jamb
Yadda Zaka Samu Maki 270+ A Jamb
 
Assalamu Alaikum, wadannan shawarwarine da babu shakka idan dalibi ya bisu sau da kafa to Insha Allahu zai samu gagarumin maki a jarabawarsa ta Jamb.
 
1. Ka tabbatar ka karanta littafin da Jamb suke bayarwa sosai da sosai, inda baka gane ba kayi tambaya, kada ka tsallake wuri wai don baka sani ba.
2. Ka tabbatar kayi Register akan lokaci, wannan zai baka dama kayi jarabawarka akan lokaci, sannan wajen register kayi nazari sosai kar ka cike ko aciki maka abinda bashi kake bukata ba.
3. Ka duba syllabus da suka baku na wuraren da za’a yi muku tambayoyi akai ka tabbatar ka bibiyesu sosai da sosai.
4. Ka tsara time table din karatu lokaci kaza zaka yi kaza lokaci kaza zaka yi kaza.
5. Ka tabbatar kana da sanayya akan computer musamman bangaren yadda ake zana jarabawa, idan baka sani ba ka nemi littafi na mai suna “Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jarabawar Jamb”
Rubutuka Masu Alaka:
6. Ka tabbatar Registration Slip din ka yana hannun ka sannan kayi kwafi din sakamar guda biyu a hannunka,
7. Ka tabbatar kayi gwajin jarabawar a na’ura mai kwakwalwa musamman idan baka da kwarewa akan Computer,
8. Ka ziyarci cibiyar da aka tura ka domin zana jarabawa ka tabbatar da yankin da take yanda ranar jarabawa zaka iya kai kanka kai tsaye ba tare da kwatance ba don gudin makara,
9. Ka tabbatar da Rana da kwanan wata da aka saka zaka yi jarabawar da lambar kujerar da zaka zauna,
10. Ka tabbatar da lokacin da safe ne ko da yamma kuma karfe nawa ne? mafi kyau ka kasance a inda za kayi jarabawa awa daya kafin lokacin jarabawar domin tantacewa,
11. Ka tanadi Fensir, Biro da kuma Shafana
12. Ka halarci cibiyar da zakayi jarabawa akan lokaci
13. Ka tabbatar an tantance ka ta kafin jarabawa da bayan kammala jarabawa
14. Kabi dukkan sharuda da ka’idoji da za’a gabatar muku a wajen
15. Kada ka danna Computer har sai an bada umarni
16. Ka nustu sosai domin amsa tambayoyin, don gudun rikicewa a yayin jarabawa
17. Kada kayi “Refresh” na Computer din ko ka danna “Submit” har sai ka kammala jarrabawa,
Basheer Sharfadi
CEO Sharfadi.com
20-09-2018
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!