Kayi Apply Yanzu: Tallafin Karatu Na Gidauniyar KPMG 2018

Home WAEC Kayi Apply Yanzu: Tallafin Karatu Na Gidauniyar KPMG 2018
Kayi Apply Yanzu: Tallafin Karatu Na Gidauniyar KPMG 2018

Gidauniyyar KPMG tana gudanar da ayyukanta a kasashe 154 daga cikin kasashen duniya, karkashin ayyukan da ta sabayi na bunkasa cigaban al’umma ta samar da ayyukan yi ga mutane sama da dubu dari biyu 200,000. a yanzu haka ta bude damar bada tallafin karatu ga dalibai ‘yan Nigeria.

ABINDA KAKE BUKATA DOMIN NEMAN WANNAN SCHOLARSHIP DIN SHINE:

 1. Wanda yayi shekara biyu da kammala makarantar Secondary.
 2. Ana bukatar wanda ya samu Credit biyar 5 hade da Maths da English a SSCE (WAEC)
 3. Wanda Ya Samu 230 a Jamb da Post UTME
 4. Sannan Ya zama ka samu admission Letter daga daya daga cikin jami’o’in kasarnan.

YADDA AKE YIN APPLY SHINE:

Zaka aika da bayanan ka ta email dinsu NG-FMCareers@ng.kpmg.com

BAYANAN DA ZAKA TURA MUSU SUNE:

 1. Suna
 2. Adireshi
 3. Lambar Waya
 4. Adireshin Email
 5. Sakamakon Jarabawar SSCE (WAEC)
 6. Sakamakon Jamb/PostUTME
 7. Admission Letter
 8. Register Haihuwa.

Note:

Subject din da zaka saka wajen tura Email din shine: KSP2018 zaka iya karawa da sunanka.

Domin karin bayani zaka iya ziyartar site dinsu http://www.home.kpmg.com

Za’a rufe ranar 21, September, 2018.

YADDA AKE TURA SAKO TA EMAIL:

 1. Ka bude email dinka
 2. Sai ka danna “Compose Mail”
 3. Wajen “To” sai ka saka Email din da zaka tura sakon NG-FMCareers@ng.kpmg.com
 4. Wajen “Subject” shima sai ka saka KSP2018 zaka iya karawa da sunanka.
 5. Akwai wajen “Attach” nan zaka shiga sai ka saka hotunan wadancan takardu naka, da aka yi bayani a sama.
 6. Sai ka danna “Sent” Shikenan.
Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!