Kamfanin Google Zai Bada Horo Ga Daliban Jami’ar Bayero

Home BUK Kamfanin Google Zai Bada Horo Ga Daliban Jami’ar Bayero
Kamfanin Google Zai Bada Horo Ga Daliban Jami’ar Bayero

Kamfanin Google Zai Bada Horo Ga Daliban Jami’ar Bayero Dake Kano

Kungiyar dalibai ta kasa (SUG) reshen jami’ar Bayero dake Kano, na sanar dalibai cewa tayi hadin gwiwa na musamman da kamfanin google domin bada horo ga daliban jami’ar mai taken *GOOGLE DIGITAL SKILLS FOR AFRICA TRAINING PROGRAM*

Google zai bada horo ga dalibai guda dubu goma 10,000 acikin kwanaki uku 3.

Za’a bada horo a bangarori da dama ciki harda harkar tallace-tallace.
Za’a bada certificate cikin awanni 24 bayan taron.
Kungiyar dalibai zata dauki nauyin ci da shan dalibai a yayin taron.

*Za’a gabatar da wannan taro kamar haka:*
Rana: Laraba, Alhamis, da Jumu’a, 12, 13, 14, September, 2018
Wuri: Dakin Taro Na Al’amuran Dalibai Dake Sabuwar Jami’ar Bayero.
Lokaci: 10:00 zuwa 12:00 na rana.

Allah Ya Bada Ikon Halarta.

Mun samu sanarwa daga kungiyar dalibai ta kasa reshen jami’ar Bayero.
12-09-2018.

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!