Africa Initiative For Governance (AIG) Scholarships Za’a Rufe 14-09-2018

Home Scholarships Africa Initiative For Governance (AIG) Scholarships Za’a Rufe 14-09-2018
Africa Initiative For Governance (AIG) Scholarships Za’a Rufe 14-09-2018

Abubuwan Da Ake Bukata Domin Samun Wannan Scholarships Sune:

 1. Ka zama dan Nigeria ko Ghana
 2. Shekara 25 zuwa 35
 3. Wanda yake Degree ana bukatar First Class, ko Strong upper second class, ko kuma ya riga ya kammala Degree dinsa.
 4. Ga mai bukatar ya samu scholarships a USA ana bukatar ya kasance yana da GPA 3.7 acikin 4.0.

Abubuwan Da Ake Bukata Domin Nema Sune:

 1. CV dinka
 2. Cikakken bayanin karatunka na shekara (full academic transcript)
 3. Takardun Karatunka, da sauran shaidar kwarewarka a wasu bangaren
 4. Zaka rubuta bayanin akan ka cikin harshen turanci cikin kalmomi (1500) wanda ya kunshi bayani kamar haka:
  1. Me yasa kake son samun scholarship?
  2. Ka taba samun wata matsala a karatunka?
  3. Idan ka samu wannan scholarships kaje kayi karatun menene fatanka?
 5. Da Hotuna (passport) guda biyu.

Domin neman wannan scholarships sai ka shiga http://aigscholarships.org/Mobile/Account/Register

 

Za’a rufe ranar Jumu’a 14 September 2018.

 

 • Idan ka cike za’a tura maka da sako ta email dinka inda zaka bi ka cigaba da cikewa, don haka ka kula da kyau kada ka sanya email dinka ba dai-dai ba.
 • Idan ka shiga sakon da suka tura maka ta email zasu baka dama sai ka danna “Continue application” sai kayi login.
 • Idan ka na da wata matsala kai tsaye zaka iya tuntubarsu ta email a helpdesk@aigafrica.org
 • Hoton da zaka yi uploading girmansa ana bukatar ya zama 50kb.

 

Abinda Yakamata Ka Sani:

Idan AIG suka baka Scholarships bayan ka gama zasu baka damar aiki dasu a kasarka na mafi karanci shekara 3 daga nan ne idan mutum yana ganin zai cigaba da aiki dasu, kuma sun gamsu dashi sai ya cigaba idan kuma zai nemi wani aikin ne shikenan.

 

Shiga Nan Domin yin like na shafin mu na facebook

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!