YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABARWAR WAEC 2018

Home Exam's YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABARWAR WAEC 2018
YADDA AKE DUBA SAKAMAKON JARABARWAR WAEC 2018

Taba Ka Lashe 007

Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabarwar WAEC 2018

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu, a darasin mu na bakwai mai taken taba ka lashe za muyi magana akan yadda ake duba sakamakon jarabarwar #WAEC ta wannan shekara.

Kamar shekarar da ta gabata a bana ma dalibi bashi da bukatar siyar Scratch Card domin duba Jarrabawar WAEC zai yi amfani ne da katin jarrabawarsa amadadin Scratch Card.

Yadda Zaka Duba Sakamakon Ka

  1. Da farko zaka ziyarci shafin yanar gizo-gizo wanda ake duba sakamakon a can mai adireshi kamar haka :

https://www.waecdirect.org

  1. Sai ka sanya lambar jarrabawa WAEC dinka a gida na farko. (lambobi guda 7 na cibiyar (centre) din da kayi Jarrabawar sai kuma lambobi guda 3 na Jarrabawar ka ma’ana lambobi guda 10 zaka shigar.
  2. Sai ka zabi shekarar da kayi Jarrabawar a gida na biyu.
  3. Sai ka zabi irin Jarrabawar da kayi ma’ana Private ce ko kuma irin tamu? (School Candidate Results)
  4. Sai ka sanya Serial Number din dake jikin katin Jarrabawar ka.
  5. Sannan ka sanya PIN din dake jikin katin Jarrabawar ka.
  6. Sai ka danna “Submit” ka jira ya danyi loading kadan zai nuno maka sakamakon ka.

Allah Ya Baiwa ‘Yan Uwa Dalibai Sa’a Amin.

#BasheerSharfadi #WAEC2018
Email: info@sharfadi.com
Call & WhatsApp: 09035830253
Website: www.sharfadi.com

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!