[Jamb] KARANTA YADDA ZA’A FARA JARRABAWAR JAMB

Home Exam's [Jamb] KARANTA YADDA ZA’A FARA JARRABAWAR JAMB
[Jamb] KARANTA YADDA ZA’A FARA JARRABAWAR JAMB

Wannan hoton dake kasa irin sa ne kowane dalibi zai gani akan computer din da zai zana jarabawa:

Kamar yadda kuke gani a hoton shine inda ake saka Reg. No sannan yana karewa ne da Harufa biyu kuma da manyan baki, bayan ka saka sai ka danna Login
Bayan ka danna login zai nuna maka irin wannan hoton da kake gani a kasa sunan ka, hotonka da Reg. No da Subject din da zakayi jarabawa a kansu,
Note: Idan kaga an saka maka subject din da bashi kayi register ba nan take ka sanarwa da masu kula da jarabawar,
daga nan sai ka danna “start exam” ma’ana fara jarabawa shikenan zai yi loading kadan kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa,
Daga nan zai bude maka jarabawar kamar hoton da zaizo a kasa tambaya da kuma amsoshin ta sai ka zaba sannan a sama yana nuna maka lokaci yana tafiya,
Kamar Yadda kuke iya gani a hoton ga bangarori nan daban da ya wajaba ko wane dalibi ya sansu da kuma amfanin su,
Idan dalibi yabi wadannan matakai ya kammala jarabawar sa to abu na karshe shine “submit” wanda hakan yake nuna cewa ya gama zana Jarabawar sa, kamar yadda kuke gani ga alamar “submit” nan, sai dai wani hanzari ba gudu ba kada kayi kuskuren danna “Submit” ko kuma wani abu da dalibai suke yi na danna “submit” bayan sun gama amsa subject misali sun gama English sai suyi submit in sun gama History ma sai suyi to idan mutum yayi haka yana nufin iya tambayoyin da ya fara amsawa yayi submit to sune kadai wadanda ya amsa.

Idan ka tabbatar ka kammala sai ka danna submit zai fito ma da hoto kamar haka:
Ka tabbatar kana so ka kammala jarabawar ka? Sai ka danna “Yes” ma’ana “Eh” daga nan sai a jira cikin kankanin lokaci ko kasa da yini guda zaka ga an turo maka da sakamakon ka.

Bam-bamcin Jamb ta Bana da sauran shekaru na baya:
1. Zaka amsa duka tambayoyin acikin awa biyu (2) mai makon (3),
2. Use of English: tambayoyi guda (60) ne mai makon (100)
3. Sauran subject guda (3) ko wanne tambayoyi (40) ne mai makon (50),
4. Gabaki daya dalibi zai amsa tambayoyi guda (180) ne mai makon (250)
Anan zan gimtse wannan rubutu nawa tare da fatan Alkhairi da fatan samun nasara ga dukkan yan uwana dalibai da zasu zana wannan jarabawa, naku a koda yaushe:

RUBUTUKA MASU ALAKA:

Littafi Kyauta Ga Daliban da Zasu Zana Jarrabawar Jamb 2019

Yadda Zaka Samu Maki 270+ A Jamb

[Jamb 2019] Bayan Kammala Register Ko Yaushe Za’a Fara Cirar Jamb e-Slip?

[Jamb 2019] Yadda Zaka Canja Jamb Dinka Zuwa D.E

[Kayi Download Yanzu] Syllabus Na Jamb 2019

[Karanta Yanzu] Dalilin Da Yasa Dalibi Zaici Jamb Amman Ya Rasa Samun Admission

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!