YADDA AKE SHIGA TSARIN NPOWER

Home Jobs YADDA AKE SHIGA TSARIN NPOWER
YADDA AKE SHIGA TSARIN NPOWER

(SHIN YAYA ZAN DUBA SUNA NA? SANNAN YAYA SABO ZAI NEMA?)

A daren jiya ne aka saki sunayen wadanda suka yi nasara a tsarin nan na bada tallafi domin magance matsalar rashin aikin yi na gwamnatin tarayya mai lakabin Npower, sai dai tun daga jiyan da yawa daga al’ummar mu na hausawa na tayi tambayoyi dangane da abinda ya shige musu duhu akan wannan batu, hakan yasa nayi wannan rubutu domin yin bayani akan sa domin dai mu gudu tare mu kuma tsira tare,

1. Ga sababbin masu neman shiga cikin shirin Npower ina basu shawara da suje #Cafe mafi kusa da su domin cike musu idan kuma zasu iya yi ta wayoyin su na zamani ma’ana mutum yana da kwarewa akai to zai je www.npower.gov.ng shine shafin da ake yin wannan register idan kaje zaka zabi bangaren da kake son cikewa,

2. Hanyoyin da ake bi wajen duba sunayen da aka saki sune kamar haka:

1) Ka ziyarci http://www.npower.gov.ng/n-power/check sai ka sanya lambar wayar ka ko email dinka ko kuma BVN din ka a akwatin bincike (searching) idan har kayi nasarar shiga zaka ga cikakken sunan ka ya fito daga nan kuma zasu tura maka sako ta waya (sms) sai ka shirya tantancewa wadda ranar da za’a yi ta zai zo a kasa,

2) Hanya ta biyu:

a. ka ziyarci www.npower.gov.ng kayi “login”
b. sai ka dannan “check your pre-selection status”.
c. sai ka sanya lambar wayar ka, ko email dinka ko kuma BVN din ka a akwatin bincike wajen (searching) idan har kayi nasarar shiga zaka ga cikakken sunan ka ya fito,
d. daga nan kuma zasu tura maka sako ta waya (sms) da kuma na (email|) na taya murna da yin nasara a zagaye na farko,
e. daga nan sai ka shirya tantancewa ta gaba da gaba wadda za’a gabatar daga ranar 27th November zuwa 8th, December 2017.

Note: Ga hoton wannan hanyoyin da ake bi nan a kasan postin din sannan akwai hoton lambobin da Npower suke kiran mutane dasu domin gudun yan cuwa-cuwa idan kaga an kira ka da lamba sabanin wadannan sai ayi taka tsan-tsan.

Domin Karin haske akai a iya tuntuba ta:
Email: info@sharfadi.com
Facebook: www.facebook.com/journalistsharfadi
Twitter: www.twitter.com/bjournalist55
Instagram: www.instagram.com/journalist55
Phone Number: 09035830253
sharfadi.com #BasheerSharfadi #Npower

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!