Mecece Jarrabawar Jamb? Da Kuma Tarihinta

Home Exam's Mecece Jarrabawar Jamb? Da Kuma Tarihinta
Mecece Jarrabawar Jamb? Da Kuma Tarihinta

TABA KA LASHE 001
Gabatarwa:
Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuhu, wannan takardar ce da zata kunshi muhimman bayanai dangane da Jarabawar Jamb tun daga ma’anar ta, tarihin ta, da Sharudanta da kuma yadda ake yinta, me kuma ake bukata idan za’ayi ta ? sannan me yasa ake yin ta.
Cibiyar Sunnah News Nigeria itace ta shirya wannan takarda domin amfanar daliban da zasu zana jarabawar a wannan karon da wadanda zasu zo nan gaba domin dai ganin an gudu tare an kuma tsira tare.
Cibiyar ta zabi harshen Hausa domin yin rubutun akai domin ‘yan uwan mu hausawa masu karancin kwarewa a yaren turanci su samu damar amfana da ita, kuma an yi takardar ne domin amfanin su, masana sun hadu akan irin yadda harshen uwa yake da matukar tasiri wajen isar da sako don haka muka ga mafi dacewa kuma mafi taimako ga dalibai na yankin da muke ciki shine muyi amfani da harshen hausa domin isar da sakon cikin kankanin lokaci, sai ku biyo mu.
Sharadi:
Ba’a yarda wani ko wata tayi amfani da wannan takarda ko tayi kwafi dinta ba tare da iznin marubucin ba.

Mecece Jarabawar Jamb?
Jarabawar Jamb Jarabawa ce da dalibai ke yinta domin neman samun gurbin karatu a jimi’o’I da kwalejoji da kuma makarantun kimiya da fasaha wadda wata hukuma da ake kira da JOINT ADDMISSION AND MATRICULATION BORD (JAMB) take shiryawa kuma ake kiran jarabawar da sunan hukumar ana yin ta sau daya (1) a shekara akwai adadin makin da ko wace makaranta take bukatar mai neman shigar ta ya samu,
Jarabawar tana da wasu ka’idoji na sai mutum ya na da sakamakon jarabawar karshe ma’ana ya gama Sakandire ko kuma yana Shekarar karshe wadanda ake kiran su da WAITING RESULT a turance ma’ana wadanda ke zaman tsammanin jiran ganin sakamakon jarabawar su suma ba’a barsu a baya ba sukan zana wannan jarabawar tare da fatan in an dace sai ayi tazarce kai tsaye zuwa makarantun gaba da sakandiren,

Tarihin Jamb
A shekarar 1974 lokacin a kasar nan ana da a jami’o’I guda bakwai (7) kuma ko wacce tana tsara yin jarabarwar neman shigarta ne akaran kanta ga daliban dake da sha’awar shiga, sai a cikin shekarar 1976 zamanin mulkin soja na Olusegun Obasanjo aka samu Karin jami’o’I guda shida (6) sannan aka fara tunanin yadda za’a maida yin jarabawar neman shiga makarantun gaba da sakandire bai daya a lokacin ne gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai tsara da kuma lura da yadda al’amuran zasu kasance kar-kashin Mr. M. S. Angulu,

An kirkiri hukumar shirya jarabawar Jamb a shekara ta 1978 sannan an yi wa hukumar garanbawul a shekarar 1989 da 1993 duka wadannan lokuta ana yin jarabawar ne a takarda a shekarar 2009 hukumar ta fuskanci matsaloli agame da jarabawar hakan yasa a shekarar 2013 akayi wani kwarya-kwaryar canji na tsarin gudanar da jarabawar inda aka koma amfani da Computer wajen gudanar da ita saboda wasu dalilai da zasu zo a gaba,

Domin karin haske ko shawarwari ko aiko da wani batu da kuke son a tattauna akai sai a tuntubi:
Phone Number: 09035830253
Email: bjournalist55@hotmail.com
Facebook: www.facebook.com/journalistsharfadi
Twitter: www.twitter.com/bjournalist55
Instagram: Journalist55

Basheer Journalist Sharfadi

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!