[Jamb] Me yakamata nayi kafin ranar jarabawar Jamb?

[Jamb] Me yakamata nayi kafin ranar jarabawar Jamb?

Ka tabbatar Registration Slip din ka yana hannun ka sannan kayi kwafi din sakamar guda biyu a hannunka,

 1. Ka tabbatar kayi gwajin jarabawar a na’ura mai kwakwalwa musamman idan baka da kwarewa akan Computer,
 2. Ka ziyarci cibiyar da aka tura ka domin zana jarabawa ka tabbatar da yankin da take yanda ranar jarabawa zaka iya kai kanka kai tsaye ba tare da kwatance ba don gudin makara,
 3. Ka tabbatar da Rana da kwanan wata da aka saka zaka yi jarabawar da lambar kujerar da zaka zauna,
 4. Ka tabbatar da lokacin da safe ne ko da yamma kuma karfe nawa ne? mafi kyau ka kasance a inda za kayi jarabawa awa daya kafin lokacin jarabawar domin tantacewa,

ME YAKAMATA NAYI A RANAR JARABAWA?

 1. Ka tanadi Fensir, Biro da kuma Shafana
 2. Ka halarci cibiyar da zakayi jarabawa akan lokaci
 3. Ka tabbatar an tantance ka ta kafin jarabawa da bayan kammala jarabawa
 4. Kabi dukkan sharuda da ka’idoji da za’a gabatar muku a wajen
 5. Kada ka danna Computer har sai an bada umarni
 6. Ka nustu sosai domin amsa tambayoyin, don gudun rikicewa a yayin jarabawa
 7. Kada kayi “Refresh” na Computer din ko ka danna “Submit” har sai ka kammala jarrabawa,

YAYA ZANYI AMFANI DA COMPUTER DOMIN ZANA JARABAWAR?

Abubuwan da zakayi amfani dasu wajen zana jarabawar a Computer sune:

 Keybord (madannan kwamfiyuta)
1. Alphabetic (Haruffa)
2. Numeric (Lambobi)
3. Directional arrow keys (kibiyoyin zirga-zirga),

 Mouse: ana amfani dashi wajen yin kasa ko kuma sama ko tafiya tambaya ta gaba ko dawowa ta baya,

YADDA ZAKAYI JAMB BA TARE DA AMFANI DA MOUSE BA

 1. Amsohin duka zasu kasance ne “A, B, C, D” idan “A” ce sai ka danna harafin A haka ma sauran harufan,
 2. Harafin “N” domin tafiya tambaya ta gaba,
 3. Harafin “P” domin komawa tambayar baya,
 4. Harafin “S” domin kammala jarabawa “submit”
 5. Harafin “R” domin dawowa ga jarabawa,
 6. Harafin “C” domin cigaba da jarabawa,

Phone Number: 09035830253
Email: info@sharfadi.com
Facebook: www.facebook.com/journalistsharfadi
Twitter: www.twitter.com/basheersharfadi
Instagram: www.instagram.com/basheer_sharfadi

YouTube: www.youtube.com/BasheerSharfadi#BasheerSharfadi

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!