JAMB TA WANNAN SHEKARAR 2018

Home Exam's JAMB TA WANNAN SHEKARAR 2018
JAMB TA WANNAN SHEKARAR 2018

TABA KA LASHE 002
JAMB TA WANNAN SHEKARAR 2018
Yanzu kuma yar uwa da dan uwa bara mu kutsa cikin batun Jarabawar Jamb din ta wannan shekara wadda muke magana akan ta,
INA SON ZAN YI JARABAWAR JAMB SHIN ME YAKAMATA NAYI?
Dalibin da yake son zana jarabawar jamb a wannan shekara 2018 zai bi matakai kamar haka:

i. Dalibi ya mallaki email account (wanda yake yin amfani dashi) sannan ya bude Jamb Profile wanda ake budewa a www.jamb.org.ng sannan yayi printing din (jamb profile details) bayanan profile din nasa wanda zasu turo masa ta email din sa
ii. Zai tafi da copy Jamb Profile din banki sannan ya biya N 5,500 ka tabbatar ka rike tailer din da ka biya gudun samun bacin rana, bankin zasu baka (Jamb Pin) wasu bankunan sukance ka koma washe gari bayan ka biya, sannan baya ga wannan hanyar ma ana iya biya online idan ka karbi wannan Pin din dashi zaka je cibiyoyin da ake yin jarabawar Jamb din domin suyi maka register anan za’a cike maka courses din da kake son yi, ko wane dalibi sai yayi jarabawar English sai kuma subject guda uku da suka shafi bangaren da yake so yayi karatu akai ana yin wannan register ne akan kudi N 700 daga nan zasu baka takarda mai kunshe da bayanan register din daka yi sannan su baka Plate mai kunshi da bayanai akan jarabawar jamb da kuma bangarorin da ake sa ran yin tambayoyi akai da sauran bayanai, sannan za’a baka littafin da zaka karanta wanda jamb suke bayarwa duk shekara a wannan shekara an bayar da littafi mai suna INDEPENDENCE wallafar Sarah Ladipo Manyinka,
iii. Daga nan sai ka jira su fara aiko da sakon inda zakayi jarabawa da lokaci da lambar mazauni wanda a turance ake kiran wannan takarda da (Slip) ,
iv. Daga nan ya rage na dalibi yaje ya koyi yadda ake sarrafa computer wajen yin jarabawar sannan ya dage da karatu da yin addu’ar samun nasara,

JAMB CBT TRAINING ( Jamb Computer Basic Test)
Jamb CBT Training wanda a hausan ce muke cewa bada horo ko gwajin yadda dalibi zai zana jarabawar Jamb da Computer an fara yin sa ne a shekarar 2013 sakamakon maida yin jarabarawar Jamb da Na’ura mai kwakwalwa inda ake nunawa dalibai yadda ake amfani da na’urar da kuma abubuwan da ya kamata mutum ya kiyaye yayin jarabawar,

AMFANIN YIN JAMB A COMPUTER
i. Samun Sakamako cikin kankanin lokaci,
ii. Magance matsalar rashin samun cikakken sakamako,
iii. Magance satar jarabawa,

Domin karin haske ko shawarwari ko aiko da wani batu da kuke son a tattauna akai sai a tuntubi:
Phone Number: 09035830253
Email: bjournalist55@hotmail.com
Facebook: www.facebook.com/journalistsharfadi
Twitter: www.twitter.com/bjournalist55
Instagram: Journalist55
Basheer Journalist Sharfadi
#BasheerSharfadi

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

Leave a Reply

Your email address will not be published.

error: Content is protected !!